Wednesday, June 10, 2026
HomeLabaraiJirgin Ƙasan Kaduna–Abuja Ya Samu Tangardar Na‘ura a Rijana

Jirgin Ƙasan Kaduna–Abuja Ya Samu Tangardar Na‘ura a Rijana

Fasinjoji da dama sun shafe sa’o’i suna jiran gyara bayan jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja da ya samu matsala a kusa da kauyen Rijana a ranar Litinin.

 

Rahotanni daga Daily Trust sun ce jirgin ya tashi daga Kaduna da misalin karfe 2:30 na rana, amma ya lalace a hanya, lamarin da ya jinkirta tafiyar da aka saba kammalawa cikin kusan sa’o’i biyu da rabi.

 

Majiyoyi sun ce matsalar ta tilasta wa jirgin tsayawa na dogon lokaci yayin da aka yi kokarin gyara shi kafin a ci gaba da tafiya.

 

Manajan tashar jirgin kasa ta Abuja na Hukumar NRC, Mista Modibbo, ya tabbatar da faruwar lamarin a sakon WhatsApp da ya aike ranar Litinin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments