Wednesday, June 24, 2026
HomeLabaraiMutane 23 Sun Mutu, Sama da 100 Sun Jikkata a Harin Bama-bamai...

Mutane 23 Sun Mutu, Sama da 100 Sun Jikkata a Harin Bama-bamai a Maiduguri

‎Aƙalla mutane 23 sun mutu, yayin da mutane 108 suka jikkata sakamakon wasu jerin fashewar bama-bamai da suka auku a daren Litinin.

‎Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta ce hare-haren sun faru ne a wurare masu cunkoso, ciki har da kasuwar Monday Market, ƙofar asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri da kuma gadar sama ta Post Office.

A rahoton da Nigerian Post ta samu, ‎Mai magana da yawun rundunar, Nahum Kenneth Daso, ya ce an yi amfani da na’urorin fashewa na IED, yana mai cewa an kai hare-haren ne a lokaci guda a wurare daban-daban.

‎Jami’an tsaron dai sun killace yankunan tare da fara bincike, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci.

‎Kwamishinan ’yan sanda, Naziru Abdulmajid, ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa, tare da tabbatar da ƙara tsaurara matakan tsaro.

‎Hukumomi sun buƙaci al’umma su kasance cikin lura tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments