Tuesday, October 27, 2026
HomeLabaraiAn Kwantar da Dalibai 64 Asibiti Bayan Shan Maganin Rigakafin Tsargiya a...

An Kwantar da Dalibai 64 Asibiti Bayan Shan Maganin Rigakafin Tsargiya a Katsina

Dalibai kimanin 64 na wata makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati da ke ƙaramar hukumar Batagarawa a jihar Katsina, sun kwanta asibiti bayan Maganin da suka Sha na inganta lafiyar su ya canja ma su wani Yanayi na daban, sakamakon shan wani magani da aka raba musu a makarantar.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Lamarin ya faru ne ranar Litinin, inda daliban suka fara fama da amai, jiri da ciwon ciki. Wasu daga cikinsu ma an kai su asibiti a sume.

An garzaya da daliban zuwa Babban Asibitin Kwararru na Janar Amadi Rimi da ke Batagarawa, da kuma wasu asibitoci da suka haɗa da Babban Asibitin Katsina da Asibitin Turai Yar’Adua.

Daraktan lafiya na asibitin, Dakta Auwal Sani, ya tabbatar da cewa sun karɓi daliban da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, bayan da suka fara nuna alamun rashin lafiya sakamakon shan maganin da ake zargin na rigakafin cutar tsutsar ciki ta schistosomiasis ne.

Ya ce ma’aikatan lafiya sun yi gaggawar ba su magungunan da suka dace, ciki har da magungunan kashe ƙwayoyin cuta, masu rage raɗaɗi da hydrocortisone.

Sai dai bayanan da wasu daliban suka bayar sun haifar da tambayoyi kan yadda aka raba maganin da kuma ko an tilasta musu shansa.

Wani ɗalibi a makarantar, Abubakar Muhammad Khairi, ya shaida cewa, wasu mutane sun shiga ajinsu da misalin ƙarfe 11 na safe, inda suka fara raba musu ƙwayoyin magani bayan sun auna tsawonsu.

Ya yi zargin cewa adadin ƙwayoyin da aka ba kowane ɗalibi ya danganta da tsawonsa, sannan aka yi barazanar dukan waɗanda suka ƙi shan maganin za a yi ma su duka.

“Idan ka ƙi shan maganin, za su buge ka. Bayan dukkanmu mun sha maganin, ɗalibai suka fara faɗuwa,” in ji shi.

Khairi ya ce an sanar da su cewa maganin na Rigakafin cutar tsargiya ne, wadda ya danganta da fitar jini a cikin fitsari, duk da cewa shi ba ya fama da matsalar.

Ya ƙara da cewa ya sha maganin ne saboda tsoron kada a buge shi idan ya ƙi.

Shi ma wani ɗalibi, Hassan Muhammad, ya ce lamarin ya faru ne bayan sun dawo daga hutun karin kumallo, lokacin da suke gudanar da darussa.

A cewarsa, mutumin da ya shiga ajinsu ya sanar da su cewa za a ba dukkan ɗalibai maganin, ko da suna fama da cutar da ake zargin maganin na yi wa aiki ko ba sa fama da ita.

Hassan ya ce an raba ƙwayoyin maganin bisa tsawon ɗalibai, inda shi ya sha ƙwayoyi uku kafin ya fara jin rashin lafiya.

Ya kuma ce mutumin da ya raba maganin ba malamin makarantar ba ne, kuma bai zo tare da malamai ba, sai dai ya zo tare da shugabannin ɗalibai da aka fi sani da prefects.

A nasa ɓangaren, Ma’aruf Abdullahi Sani, wani uba daga ƙaramar hukumar Katsina, ya ce ’ya’yansa uku da ke makarantar duk sun sha maganin, amma ɗaya ne ya samu matsala mafi tsanani.

Sai dai ya ce tun daga lokacin, yaran sun samu sauƙi sosai.

Da yake magana a asibitin, Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare na jihar Katsina, Hon. Yusuf Suleman Jibiya, ya ce gwamnatin jihar za ta gudanar da bincike domin gano yadda aka raba maganin ga ɗaliban.

Ya ce ma’aikatar ta samu labarin faruwar lamarin ne, wanda hakan ya sa suka garzaya asibitin domin duba halin da ɗaliban ke ciki.

Ya tabbatar da cewa lafiyar ɗaliban ta daidaita, inda ya ce ana shirin ba su abinci kafin a mayar da su makaranta.

Dangane da wanda ya kawo maganin makarantar, Jibiya ya ce za a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

A lokacin haɗa wannan rahoto, har yanzu ba a bayyana wanda ya kawo maganin makarantar, wanda ya ba da izinin raba shi, ko kuma ainihin sunan maganin da adadin da aka bai wa kowane ɗalibi ba.

Haka kuma, ba a tabbatar da ko an gudanar da rabon maganin ne bisa izinin hukumomin lafiya da sauran hukumomin da abin ya shafa ba.

Maganin praziquantel dai, na daga cikin magungunan da ake amfani da su wajen magance cutar schistosomiasis, wadda aka fi sani da cutar tsutsar jini. Haka kuma, ana amfani da shi a shirye-shiryen yaƙi da cutar a wuraren da ta zama ruwan dare.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da cewa wannan ne maganin da aka bai wa ɗaliban ba, ko kuma adadin da suka sha ya dace da yanayin lafiyarsu ba.

Ana sa ran binciken gwamnatin jihar zai gano yadda maganin ya shiga makarantar, wanda ya ba da izinin raba shi, da kuma ko an bi ƙa’idojin kula da lafiyar ɗalibai wajen gudanar da aikin.

Lamarin ya kuma sake jawo hankula kan muhimmancin bin ƙa’idojin lafiya da samun sahihin izini kafin raba magunguna ga ɗalibai, musamman a makarantun kwana.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments