Wanda ya kafa kuma jagoran ƙungiyar Alternative Politics Movement, Otunba Segun Showunmi, ya ce cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ya zama wajibi, ganin irin halin matsin tattalin arziki da Najeriya ke ciki kafin zuwan gwamnatin yanzu a watan Mayun 2023.
Showunmi ya bayyana cewa ci gaba da biyan tallafin man fetur ba zai yiwu ba, saboda irin nauyin da yake ɗora wa baitulmalin ƙasa, alhali kuwa tsarin bai samar da sakamakon da aka tsara domin cimmawa ba.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 10 ga Nuwamba, 2026, yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) da ke Katsina.
A cewarsa, an fara aiwatar da tsarin tallafin man fetur ne tun a shekarun 1970, kafin ya samu gindin zama a kusan shekarar 1978, da nufin bunƙasa masana’antu, sauƙaƙa rayuwar al’umma da kuma ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.
Sai dai ya ce abin takaici shi ne, duk da makudan kuɗaɗen da gwamnatoci suka kashe wajen tallafa wa farashin man, ba a samu cikakkiyar nasarar manufofin da aka kafa tsarin domin cimmawa ba.
Showunmi ya yi ikirarin cewa lokacin da Tinubu ya karɓi ragamar mulki a ranar 29 ga Mayun 2023, ƙasar na cikin mawuyacin halin kuɗi, inda ya ce kasafin kuɗin da sabuwar gwamnatin ta gada bai ƙunshi tanadin da zai ba da damar ci gaba da biyan tallafin man fetur ba bayan rantsar da shugaban ƙasar.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, ya danganta jinkirin cire tallafin da gwamnatocin baya suka yi da fargabar fuskantar matsin lamba da turjiya daga al’umma, yana mai tunatar da yadda gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ta yi ƙoƙarin cire tallafin, amma ta gamu da zanga-zangar adawa daga jama’a.
Jagoran ƙungiyar ya kuma nuna damuwa kan yadda Najeriya ta kasa amfani da lokutan da take samun kuɗaɗen shiga masu yawa sakamakon tsadar ɗanyen mai a kasuwannin duniya wajen samar da ingantattun hanyoyin sufuri, ababen more rayuwa da inganta walwalar ma’aikata.
Ya ce tsarin tallafin man fetur ya kuma taimaka wajen bunƙasa safarar man zuwa ƙasashen maƙwabta, musamman Kamaru da Jamhuriyar Benin, lamarin da ya ce ya rage amfanin tallafin ga ‘yan Najeriya.
Haka kuma, ya yi tambaya kan yadda adadin man fetur da ake ikirarin ana amfani da shi a ƙasar ya kai wani matsayi, yana mai zargin cewa zamba wajen shigo da mai, amfani da takardun bogi da kuma ƙarin kuɗaɗen tallafi da ba su dace ba sun taimaka wajen jefa tattalin arzikin ƙasar cikin matsala.
Da yake tsokaci kan gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, Showunmi ya tuna da bayanin da Buhari ya taɓa yi na cewa Najeriya ƙasa ce mai fama da cin hanci da rashawa, yana mai cewa gwamnatin da ta gabata ta gaji matsaloli masu yawa na tattalin arziki da tsarin hukumomi.
Ya ce ƙarancin kuɗaɗen shiga ya shafi ikon gwamnati na samar wa sojoji kayan aiki, gudanar da ayyukan raya ƙasa da kuma biyan wasu muhimman buƙatun ƙasa.
Ya kuma yi nuni da irin matsalolin da gwamnatocin jihohi suka fuskanta wajen biyan albashi da fansho, inda tallafin kuɗi daga gwamnatin tarayya ya zama wata hanya ta yau da kullum wajen taimaka wa wasu jihohin gudanar da ayyukansu.
Don ƙarin fayyace matsalar, Showunmi ya yi amfani da misalin iyali, inda ya ce iyalin da ke ci gaba da karɓar bashi domin cike gibin kuɗin shigarta ba za ta iya da’awar tana cikin wadatar arziki ba.
Ya kwatanta wannan da yadda Najeriya ta dogara da rance da kuma kuɗaɗen da ake sa ran samu daga man fetur domin biyan buƙatun yau da kullum, yana mai cewa irin wannan tsarin ba shi da ɗorewa.
A wani ɓangare na jawabinsa, Showunmi ya kare manufofin sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa an ƙirƙiro su ne domin gyara matsalolin da suka daɗe suna hana ƙasar samun ci gaba da kuma inganta yadda ake tafiyar da kuɗaɗen gwamnati.
Ya yi iƙirarin cewa yanayin kuɗaɗen gwamnatin tarayya ya samu sauyi a ƙarƙashin gwamnatin yanzu, inda ya danganta hakan da ƙarin kuɗaɗen da gwamnati ke iya tarawa da kuma damar aiwatar da wasu shirye-shiryen raya ƙasa.
Haka kuma, ya soki tsarin musayar kuɗaɗen waje da aka riƙa amfani da shi a baya, yana mai cewa ya taimaka wajen haifar da ƙarancin dalar Amurka da kuma raunana matsayin tattalin arzikin Najeriya a idon ƙasashen duniya.
Sai dai ya amince cewa sauye-sauyen da ake aiwatarwa sun jefa ‘yan Najeriya cikin matsin rayuwa, amma ya ce matakan sun zama wajibi domin samar da ingantaccen tsarin tattalin arziki da zai iya ɗorewa a nan gaba.
Ya buƙaci jama’a da su yi la’akari da irin halin da ƙasar take ciki kafin zuwan gwamnatin Tinubu, maimakon mayar da hankali kawai kan matsalolin da suka biyo bayan sauye-sauyen.
Showunmi ya kuma bayyana shirin gwamnatin tarayya na amfani da iskar gas (CNG) wajen tafiyar da motocin haya da sauran ababen hawa a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin rage dogaro da man fetur.
Ya ce samar da motocin da ke amfani da CNG da kuma sauya injinan wasu motoci domin su dace da amfani da iskar gas na iya samar da wata hanya ta daban wajen tafiyar da harkokin sufuri.
A cewarsa, Najeriya na da albarkatun iskar gas masu yawa da ya kamata ta yi amfani da su wajen samar da hanyoyin makamashi daban-daban, domin rage matsin da ɓangaren sufuri ke fuskanta.
Ya jaddada cewa komawa ga tsohon tsarin tallafin man fetur ba tare da magance matsalolin da suka haifar da shi ba na iya sake jefa ƙasar cikin irin ƙalubalen kuɗaɗen da ta sha fama da su a baya.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya su yi haƙuri
Jagoran Alternative Politics Movement ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi haƙuri yayin da gwamnatin Tinubu ke aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, yana mai cewa irin waɗannan matakai na buƙatar lokaci kafin a fara ganin cikakken sakamakonsu.
Ya ce yana da muhimmanci gwamnati ta ci gaba da aiwatar da manufofinta domin magance matsalolin kuɗaɗen ƙasa da kuma kafa tubalin tattalin arziki mai ɗorewa.
Haka kuma, ya shawarci ‘yan siyasar da ke gabatar da wasu hanyoyin tafiyar da tattalin arziki da su bayyana yadda za su samar da kuɗaɗen aiwatar da manufofinsu, tare da fayyace yadda za a ci gaba da ɗaukar nauyinsu ba tare da ƙara jefa gwamnati cikin matsin kuɗi ba.
Showunmi ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya, musamman mazauna yankin Arewa maso Yamma, da su mara wa Shugaba Tinubu baya domin samun wa’adi na biyu a zaɓen 2027.
Ya ce ci gaba da mulkin Tinubu zai ba shi damar kammala sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta fara aiwatarwa.
A ƙarshe, ya buƙaci ‘yan jarida da su riƙa gabatar da rahotanni masu zurfi da daidaito kan manufofin gwamnati da shirye-shiryen raya ƙasa, domin taimaka wa al’umma fahimtar dalilan da suka haifar da matakan tattalin arzikin da ake ɗauka.
