HomeSashen HausaAn Horar da Daliban Jinya da Ungozoma kan Hanyoyin Dogaro da Kai...

An Horar da Daliban Jinya da Ungozoma kan Hanyoyin Dogaro da Kai a Katsina

-

Gidauniyar Resilience and Unity Humanitarian Foundation (RUHF) ta shirya wani taron horaswa ga daliban da ke koyon aikin jinya da ungozoma a makarantar Qasimu Kafar Bai da ke Katsina. An gudanar da taron ne a dakin taro na makarantar a ranar Alhamis, 12 ga watan Yuni, 2025, karkashin jagorancin shugaban gidauniyar, Ahmad Muhammad Nafi’u.

Tunda farko, shugaban gidauniyar ya bayyana cewa an shirya horon ne domin koya wa matasa hanyoyin dogaro da kai bayan kammala karatu, ba tare da jiran aikin gwamnati ba.

Ahmad Muhammad ya ce, “Mun hada duk masu ruwa da tsaki a wannan fanni domin su taimaka wajen koya muku dabarun fara sana’a da kuma samun goyon bayan da ya dace domin gina nasu kasuwanci.”

Ya kara da cewa akwai hanyoyi da dama da mutum zai iya bi domin dogaro da kansa, musamman ta hanyar amfani da fasahar zamani da kuma basira. Ya ce: “Ta hanyar wayar salula da kuma kwakwalwar da Allah ya hore maka, zaka iya cin gajiyar iliminka ba tare da jiran aiki daga gwamnati ba. Ba wai hannu kawai za ka iya amfani da shi ba, akwai hanyoyin zamani da za ka iya aiki daga gida kai tsaye.”

Daga karshe, ya bukaci matasa da su tabbata sun yi rijista da Hukumar Rijistar Kamfanoni (CAC) domin su samu damar amfana da tallafi da kuma bunkasa sana’o’insu bisa ka’ida.

Haka zalika, wasu jami’an bankuna da hukumomi da suka halarci taron – ciki har da Bankin Bunkasa Masana’antu (BOI), Bankin Jaiz, da CAC – sun yi jawabi kan muhimmancin gudanar da kasuwanci bisa doka da yin rijista, wanda zai bude kofar samun tallafi da ci gaba mai dorewa.

Daga cikin wadanda suka halarta akwai: Malam Bello Abubakar Imam – Daraktan School of Nursing, Aisha Nasir Yahaya, Ahmad Muhammad daga BOI, Abdullahi Umar daga CAC, Dr. Haruna Saleh Isyaku daga Asibitin FMC, Maryam Mustapha Saulawa daga RUHF, da Aminu Ahmad Muhammad.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

SAKON ƘARSHEN SHEKARA NA KATSINA TIMES: Mun Fuskanci Barazana Da Kalubale A Shekarar 2025– Inji Malam Muhammad Danjuma Katsina

Tunda farko, ya yi godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, tare da salati da aminci ga Manzon Rahama, Annabi Muhammad (SAW), iyalansa (AS) da sahabbansa (RA),...

Obi Na Shirin Shiga ADC Yayin Da Jam’iyyar Za Ta Yi Babban Taron Ta Na Ƙasa a 2026

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party (LP), Peter Obi, na dab da shiga jam’iyyar ADC, gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Wata majiya a jam’iyyar...

Most Popular