Friday, November 20, 2026
HomeLabaraiTinubu Ya Kara Yawan Jihohin da Zai Je Kamfen Zuwa 19 Kafin...

Tinubu Ya Kara Yawan Jihohin da Zai Je Kamfen Zuwa 19 Kafin 2027

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya faɗaɗa jadawalin kamfen ɗinsa na neman wa’adi na biyu a 2027, inda ya ƙara jihohin da zai ziyarta daga 12 zuwa 19, tare da cire Bauchi daga jerin wuraren da zai halarta da kansa.

Sabon jadawalin ya nuna cewa Tinubu zai halarci tarukan kamfen guda 20, ciki har da Abuja, tsakanin 24 ga Oktoba, 2026 da 13 ga Janairu, 2027.

Jihohin da aka ƙara sun haɗa da Katsina, Taraba, Zamfara, Imo da Kwara, baya ga Akwa Ibom, Jigawa da Kebbi da ya riga ya ziyarta.

A jadawalin, Tinubu zai halarci kamfen a Katsina ranar 2 ga Disamba, Kano ranar 17 ga Disamba, Taraba ranar 19 ga Disamba, Zamfara ranar 28 ga Disamba da Imo ranar 30 ga Disamba.

A shekarar 2027, zai ziyarci Adamawa, Sokoto, Kwara da Delta, kafin ya kammala kamfen ɗinsa da babban taro a Legas ranar 13 ga Janairu.

Duk da cewa APC ta tsara tarukan kamfen guda 37 a jihohi 36 da Abuja, Tinubu zai halarci guda 20 da kansa, yayin da sauran shugabannin jam’iyyar za su jagoranci sauran tarukan.

Tun da farko, Tinubu ya bayyana cewa ba zai iya halartar dukkan tarukan ba saboda nauyin gudanar da mulki da sauran buƙatun ƙasa.

Matakin ya jawo suka daga wasu ’yan adawa, ciki har da Adewole Adebayo na SDP da ƙungiyar Peter Obi Media Reach, waɗanda suka ce wajibi ne shugaban ƙasa ya gana da ’yan Najeriya domin amsa tambayoyinsu kan ayyukan gwamnatinsa.

Sai dai APC ta kare matakin, tana mai cewa babu dokar da ta tilasta wa ɗan takarar shugaban ƙasa ziyartar dukkan jihohin ƙasar kafin zaɓe.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments