Friday, November 20, 2026
HomeLabaraiTakara Tsakanin Tinubu, Atiku da Obi Rikicin Cikin-gida Ne– Sule Lamido

Takara Tsakanin Tinubu, Atiku da Obi Rikicin Cikin-gida Ne– Sule Lamido

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana takarar shugaban ƙasa ta 2027 tsakanin Shugaba Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi a matsayin wani irin “yaƙin basasa tsakanin ’yan gida ɗaya”.

Lamido, wanda tsohon ministan harkokin wajen Najeriya ne, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV ranar Alhamis.

Ya ce ’yan takarar uku sun fito ne daga tushen siyasa iri ɗaya, domin a lokuta daban-daban sun kasance a jam’iyyun PDP da APC ko kuma sansanoninsu na siyasa.

A cewarsa, fafatawar tasu tamkar rikicin cikin gida ne, don haka ba ya damuwa da wanda zai samu nasara a tsakaninsu.

Tinubu na neman wa’adi na biyu ne a ƙarƙashin APC, Atiku kuma zai tsaya takara a ADC, yayin da Peter Obi ke shirin fafatawa a ƙarƙashin jam’iyyar NDC.

A wani ɓangare na hirar, Lamido ya kare ɗansa daga sukar da ake masa kan shiga siyasa, yana mai cewa kasancewarsa ɗan tsohon gwamna ba yana nufin an hana shi amfani da haƙƙoƙinsa na kundin tsarin mulkin Najeriya ba.

Sai dai ya ƙi yin tsokaci kan zargin da ɗansa ya yi wa gwamnan Jigawa na yanzu, cewa bai yi wa al’ummar jihar wani abin a zo a gani ba, yana mai cewa ya kamata a tambayi ɗansa kai tsaye domin jin dalilinsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments