Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce ba ya damu da yawan sauya sheƙa da ake yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki ba.
Inda ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi kai tsaye a shirin Arise TV a daren Litinin, El-Rufai ya ce shugaban ƙasa mai ci yana ɗaukar matsayin cewa tuni an gama da dawowar sa karo na biyu, ganin yadda wasu gwamnoni daga jam’iyyun adawa ke sauya sheƙa zuwa APC.
Nigerian Post ta samu cewa, sai dai El-Rufa’i ya bayyana cewa Tinubu ba zai ci zaɓe ba domin sai ma yi sa’a ya zo mataki na Uku.
Haka kuma, tsohon gwamnan ya zargi gwamnatin Tinubu da halin ko in kula dangane da matsanancin halin tsaro da ƙasar ke ciki, yana mai bayyana cewa an cire Naira Biliyan 100 daga Asusun Tarayya cikin watanni 15 da suka gabata ba tare da amincewar jihohi ko majalisar dokoki ba.
Ya ce tun cikin watanni 15 da suka wuce, ana cire biliyan 100 daga Asusun Tarayya ana tura wa hukumomin tsaro, amma ba abinda ya sauya a shekarar 2024, ya ce an sace sama da mutane Miliyan 2.2, an kashe mutum 615,000. Nigeria kamar tana cikin yaƙi ne.
A cewar sa, wannan adadi ya fi na shekaru 8 na Buhari muni, kuma duk wannan ƙididdiga daga Hukumar Kididdiga ta Ƙasa ce, ba ta wani waje ba, ya ce wannan kuɗi ne da aka ɗauka daga Asusun Tarayya ba tare da amincewar Majalisar Tarayya ba, kuma hakan ya saba doka, kuma ya cancanci a tsige shugaban ƙasa, amma har yanzu ana cigaba da hakan kuma har Yanzu ba a san inda Naira Tiriliyan 1.5 ta tafi ba.
Malam El-Rufa’i, ya kuma yi tambaya shin meyasa matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara? Meyasa Gwamnati ke buƙatar al’umma su kare kansu?