Friday, June 12, 2026
HomeLabaraiHukumomin Saudiyya sun amince da binne Aminu Dantata a Madina

Hukumomin Saudiyya sun amince da binne Aminu Dantata a Madina

Gwamnatin kasar Saudiyya ta amince da binne fitaccen dan kasuwar nan na Najeriya, Aminu Dantata a birnin Madina mai alfarma.

Babban sakatare mai zaman kansa, Mustapha Junaid, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A cewarsa, za a dauki gawar mamacin ne daga Abu Dahabi ta ƙasar Dubai zuwa ƙasar Saudiyya.

Ana sa ran za a yi jana’izar ne a safiyar ranar Litinin a birnin Madina.

Alhaji Aminu Dantata, na ɗaya daga cikin hamshakan attajiran Najeriya, ya rasu a Dubai bayan ya yi fama da doguwar jinya ya rasu yana da shekaru 94 a Duniya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments