An samu gawar wani jami’in Hukumar Kwastam mai suna Lawal Tukur mai mukamin Assistant Superintendent of Customs (ASC) a ɗakin wani otel da ke cikin garin Katsina.
Rahoton Zagazola ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 15 ga Oktoba a wani Otal mai suna Murjani Hotel da ke cikin Katsina, inda mamacin ya sauka. Rahotanni sun nuna cewar ma’aikatan otel ɗin ne suka gano gawar jami’in a cikin ɗakinsa da misalin ƙarfe 8:30 na safe, sannan suka yi kiran gaggawa.
Majiyoyi daga otel ɗin sun ce an samu wasu ƙananan buhunan magunguna ko sinadarai da ake zargin ya sha a cikin kwandon shara. An gano wasu mata uku da ake zargin suna cikin otel ɗin a lokacin da lamarin ya faru: Khadija Ali mai shekaru 34 daga unguwar Dutsin-Amare a cikin birnin Katsina, Aisha Lawal mai shekaru 30 daga karamar hukumar Ingawa, da kuma Hafsat Yusuf mai shekaru 22 daga unguwar Brigade da ke Kano.
Rahotanni sun ce Khadija da Aisha ne suka kwana tare da mamacin a daren, yayin da Hafsat din daga baya ta zo ta tarar da su a otel ɗin.
An kai gawar jami’in zuwa Federal Medical Centre (FMC) da ke Katsina, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa, sannan aka ajiye gawar a dakin ajiyar gawa don yin binciken likitanci (autopsy).
Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta samu rahoton faruwar lamarin, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwar jami’in.
Daga Zagazola Makama