HomeSashen HausaAn Kammala Taron Al’adu da Wasannin Gargajiya na “Youth Business & Culture...

An Kammala Taron Al’adu da Wasannin Gargajiya na “Youth Business & Culture Games 2025” a Katsina

-

An kammala taron Al’adu da Wasannin Gargajiya na tsawon kwana biyu da ƙungiyar Muryar Matasa Initiative for Employment Development and Inclusion ta shirya a filin wasa na Muhammad Dikko, Katsina.

 

Taron, wanda aka gudanar mai taken “Youth Business & Culture Games 2025”, ya mayar da hankali kan bunƙasa kasuwancin Matasa a fannoni Uku; Kasuwanci, Al’adu da Wasanni. Rahoton da Nigerian Post ta samu, ya tabbatar da cewa, an gudanar da taron cikin tsari, nishaɗi da maida hankali kan ƙarfafa Matasa a harkokin tattalin arziki.

 

A jawabin ta na rufe taron, Shugabar, Saratu Hamidu Samaila, ta bayyana jin daɗin ta ga yadda mahalarta suka bayar da haɗin kai har aka kammala taron cikin nasara. Ta ce manufar taron shi ne nunawa Matasa masu buƙata ta musamman maza da mata su ma suna da ƙwarewa da basira kamar kowa, kuma za su iya bada gudunmuwa wajen raya tattalin arziki da zaman lafiya.

 

Ta ƙara da cewa, wannan shi ne karo na farko da suka gudanar da taron a Katsina, tare da shirin ci gaba da gudanar da shi duk shekara domin ƙarfafa gwiwar Matasa a fadin jihar.

 

A ɓangaren kasuwanci, shirin ya tanadi baje koli domin Matasa masu ƙananan sana’o’i su gabatar da kayayyakin da suka kirkira. Baje kolin ya jawo hankalin ’yan kasuwa da masu saka jari da suka halarta domin gano sabbin hanyoyin habaka tattalin arziki.

 

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, kungiyoyin farar hula, ’yan kasuwa da jama’a masu buƙata ta musamman. Sun yaba da yadda shirin ya mayar da hankali kan inganta kwarewa, gina tunani da ƙarawa Matasa ƙarfin guiwa domin shiga sahun ci gaban tattalin arziki da al’adu.

 

An kammala taron ne a ranar Talata, 9 ga Disamba 2025, inda aka fitar da Gwarazan Shekara. Daga nan aka ci gaba da bada kyaututtuka ga waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban, ciki har da Makafi, Guragu, da sauran masu buƙata ta musamman, inda aka fitar da na ɗaya, na biyu da na uku bisa tsarin tantancewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Nijeriya Ta Musanta Zargin Leken Asiri Kan Jirginta Da Ke Burkina-Faso

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta karyata jita-jitar da ke cewa jirginta kirar C-130 da ya sauka ba tare da shiri ba a Bobo-Dioulasso,...

Duniya Za Ta Fuskanci Ƙalubale, Idan Najeriya Ta Wargaje– Inji Sanata Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa a Najeriya, Kashim Shettima ya ce gwamnatin Tinubu ba za ta taɓa bari Najeriya ta ruguje a hannunta ba, komai rintsi.   Kamar yadda...

Most Popular