HomeLabarai‎Mataimakin Gwamnan Bayelsa Ya Yanke Jiki Ya Fadi Ana Tsaka Da Aikin...

‎Mataimakin Gwamnan Bayelsa Ya Yanke Jiki Ya Fadi Ana Tsaka Da Aikin Ofis

-

Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, ya yanke jiki ya fadi yayin da yake tsaka da gudanar da ayyukansa a ofis ɗinsa da ke Gidan Gwamnati, Yenagoa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

‎Shaidu daga fadar gwamnati sun ce lamarin ya faru ne ba wani manuniyar cewa yana da wata rashin lafiya, lamarin da ya jefa ma’aikatan ofishin cikin tashin hankali.

‎Rahotanni sun tabbatar da cewa an gaggauta kai Mataimakin Gwamnan zuwa Babban Asibitin Tarayya da ke Yenagoa (Federal Medical Centre) domin kula da lafiyarsa.

‎Duk da cewa hukumomin jihar ba su fitar da cikakken bayanin halin da yake ciki ba tukuna, majiyoyi sun ce likitoci suna ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da ya farfaɗo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

ADC Ta Zargi Tinubu Da Raba Kan ‘Yan Adawa Ta Hanyar NDC

Jam’iyyar ADC ta yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC na da hannu wajen ƙirƙirar sabuwar jam’iyyar NDC domin raunata haɗin...

Vinicius Jr Accused of Reporting Teammates to Madrid Chiefs

Vinicius Jr Accused of Reporting Teammates’ Issues to Real Madrid Chiefs. Reports from several European media outlets claim that Vinícius Júnior is being accused of informing...

Most Popular