HomeLabarai‎Dangote Ya Buƙaci a Binciki Shugaban NMDPRA Kan Zargin Ɓarnatar Da Kuɗaɗe...

‎Dangote Ya Buƙaci a Binciki Shugaban NMDPRA Kan Zargin Ɓarnatar Da Kuɗaɗe ‎

-

Hamshakin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote, ya yi kira da a gudanar da bincike kan Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur na Ƙasa (NMDPRA), Farouk Ahmed, bisa zargin ɓarnatar da dukiyar jama’a da kuma cutar da tattalin arzikin ƙasa.

‎Dangote ya bayyana cewa ko shi da irin arzikin da Allah ya hore masa, ba zai iya biyan kuɗin karatun sakandaren ’ya’yansa da ya haura Naira biliyan bakwai ba. Ya ce irin wannan adadi na kuɗi ya wuce tunanin biyan kuɗin makaranta a matakin sakandare.

‎Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, ya yi wannan furuci ne cikin wani bidiyo da ya raba wa manema labarai, wanda ya yaɗu a shafukan sada zumunta a ƙarshen makon da ya gabata.

‎A cewarsa, “Shugaban Hukumar Man Fetur ta NMDPRA, Farouk Ahmed, na biyan kuɗin makarantar sakandaren ’ya’yansa har dala miliyan biyar a Switzerland.”

‎Wannan furuci ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, inda da dama ke kira ga hukumomi da su yi cikakken bincike domin tabbatar da gaskiyar zarge-zargen da kuma kare muradun tattalin arzikin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

ADC Ta Zargi Tinubu Da Raba Kan ‘Yan Adawa Ta Hanyar NDC

Jam’iyyar ADC ta yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC na da hannu wajen ƙirƙirar sabuwar jam’iyyar NDC domin raunata haɗin...

Vinicius Jr Accused of Reporting Teammates to Madrid Chiefs

Vinicius Jr Accused of Reporting Teammates’ Issues to Real Madrid Chiefs. Reports from several European media outlets claim that Vinícius Júnior is being accused of informing...

Most Popular