HomeSashen HausaNijeriya Ta Musanta Zargin Leken Asiri Kan Jirginta Da Ke Burkina-Faso

Nijeriya Ta Musanta Zargin Leken Asiri Kan Jirginta Da Ke Burkina-Faso

-

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta karyata jita-jitar da ke cewa jirginta kirar C-130 da ya sauka ba tare da shiri ba a Bobo-Dioulasso, Burkina Faso, ya je aikin leken asiri a boye.

 

Runudunar ta ce rahoton karya ne kuma ba shi da tushe, tana mai jaddada cewa jirgin na kan hanyarsa ta zuwa Portugal domin gyara, kuma saukar gaggawar da ya yi ta faru ne saboda dalilan tsaro bisa ka’idojin sufurin jiragen sama na duniya.

 

Bayanai da Jaridar The Nation sun ce wata majiya a hedkwatar tsaron NAF ta ce jirgin yana dauke da dukkan takardun izini, kuma an bi dukkan matakan da doka ta tanada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

NSCDC Ta Ƙara Karfafa Hulda Da Rundunar Sojin Saman Nigeria A Katsina

Rundunar Tsaron Nijeriya ta (NSCDC) reshen Jihar Katsina tare da Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, 213 Forward Operating Base Katsina, sun ƙarfafa haɗin gwiwarsu domin...

‎Shugaban Hukumar NMDPRA Farouk Ahmed yayi Murabus Daga Mukaminsa

‎Shugaban Hukumar NMDPRA, Injiniya Farouk Ahmed, ya ajiye aikinsa, lamarin da ya buɗe sabon babi a jagorancin hukumomin da ke kula da harkokin man fetur...

Most Popular