Jam’iyyar PDP a jihar Sokoto ta yi Allah-wadai da kamawa tare da tsare tsohon gwamnan jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, tana zargin jam’iyyar APC da yunƙurin jefa dimokuraɗiyyar ƙasar cikin rudani.
A cewar wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran PDP na jihar, Hassan Sahabi Sanyinnawal, ya fitar a yau Talata, wannan kamen na daga cikin shirin cin zarafi da murƙushe ‘yan adawa a Najeriya.
“Ana wannan kame-kamen ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin samar da haɗakar jam’iyyun adawa a ƙasar domin fuskantar zaɓe mai zuwa. Wannan mataki ba zai hana mu ci gaba da ƙoƙarin kawo sauyi ba,” in ji Sanyinnawal.
Ya kuma yi kira ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da ta daina zama “karen farauta” na gwamnatin tarayya wajen cin zarafin jam’iyyun adawa.
Tun da farko, EFCC ta gayyaci Sanata Tambuwal inda ya isa ofishinta a ranar Litinin domin amsa tambayoyi. Rahotanni sun tabbatar da cewa bayan ya amsa gayyatar, hukumar ta tsare shi bisa zargin almundahanar kuɗi.