HomeSashen HausaPDP Ta Yi Tur Da Kamen Da Aka Yi Ma Tsohon Gwamna...

PDP Ta Yi Tur Da Kamen Da Aka Yi Ma Tsohon Gwamna Aminu Waziri Tambuwal

-

Jam’iyyar PDP a jihar Sokoto ta yi Allah-wadai da kamawa tare da tsare tsohon gwamnan jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, tana zargin jam’iyyar APC da yunƙurin jefa dimokuraɗiyyar ƙasar cikin rudani.

A cewar wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran PDP na jihar, Hassan Sahabi Sanyinnawal, ya fitar a yau Talata, wannan kamen na daga cikin shirin cin zarafi da murƙushe ‘yan adawa a Najeriya.

“Ana wannan kame-kamen ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin samar da haɗakar jam’iyyun adawa a ƙasar domin fuskantar zaɓe mai zuwa. Wannan mataki ba zai hana mu ci gaba da ƙoƙarin kawo sauyi ba,” in ji Sanyinnawal.

Ya kuma yi kira ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da ta daina zama “karen farauta” na gwamnatin tarayya wajen cin zarafin jam’iyyun adawa.

Tun da farko, EFCC ta gayyaci Sanata Tambuwal inda ya isa ofishinta a ranar Litinin domin amsa tambayoyi. Rahotanni sun tabbatar da cewa bayan ya amsa gayyatar, hukumar ta tsare shi bisa zargin almundahanar kuɗi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Katsina Police Received 29 New ASPs From The Nigeria Police Academy, Wudil

The Katsina State Police Command has received 29 newly posted Assistant Superintendents of Police (ASPs) from the Nigeria Police Academy, Wudil. Welcoming the officers, the...

Yawancin Fulanin Da Suke Ta’addanci Ba Su Da Addini, Ba Su San Allah Ba– Nasir El Rufa’i ‎

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, ya bayyana cewa yawancin mutanen Fulani da ake zargi da aikata ta'addanci da kashe kashe a sassa daban...

Most Popular