HomeSashen Hausa‎Rundunar ‘Yansanda Sun Daƙile Yunkurin Harin ‘Yanbindiga a Katsina, Sun Ƙwato AK‑47...

‎Rundunar ‘Yansanda Sun Daƙile Yunkurin Harin ‘Yanbindiga a Katsina, Sun Ƙwato AK‑47 Biyu da Harsasai 24

-

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu babban nasara a ranar 29 ga watan Nuwamba, 2025, bayan da ta daƙile yunƙurin wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne wajen kai hari a hanyar Kandawa zuwa Dankar a Karamar Hukumar Batsari.

‎Sanarwar ta fito ne daga jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abubakar Aliyu Sadiq, wanda ya bayyana cewa jami’an tsaro sun kwato bindigogi kirar AK‑47 guda biyu, harsasai 24, da kuma babur kirar Boxer guda ɗaya.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, ‎wannan nasara ta biyo bayan umarnin Babban Sufeton ‘Yan Sanda na Ƙasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, PhD, NPM, kan ƙara tsaurara matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin Najeriya.

‎A ranar da abin ya faru, ofishin ‘Yansanda na Batsari ya samu rahoton, gaggawa cewa, ‘yanbindiga na shirin tarar hanyar. DPO na yankin ne ya hanzarta tattara dakaru, inda suka nufi wurin. Lokacin da suka isa, jami’an sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar, inda waɗanda suka aikata laifin suka tsere saboda ƙarfin dabaru da makaman jami’an tsaro, tare da barin kayan aikinsu a wurin.

‎Bayan bincike, jami’an sun kwato duk kayan da ‘yan bindigar suka bar bindigogi biyu, harsasai 24, da babur Boxer guda ɗaya. Haka kuma sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike domin kamo sauran da suka tsere.

‎Kwamishinan ‘yansandan jihar ya yaba wa jami’an akan jarumtar da suka nuna, tare da yin kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa rundunar sahihan bayanai domin hanzarta daukar matakai cikin gaggawa.

Kazalika, ‎rundunar ‘yan sandan Katsina ta jaddada cewa za ta ci gaba da tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a kowane lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Dalilan Da Ya Sa Na Bar APC Na Koma ADC– Inji Wada Protocol

‎Tsohon hadimin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, Alhaji Mustapha Abdu Saulawa, wanda aka fi sani da Wada Protocol, ya bayyana dalilin da...

Yaron Shago Ya Hallaka Ubangidansa da Almakashi a Gombe, Kwanaki Kadan Da Aurensa

Jihar Gombe ta shiga alhini biyo bayan wani mummunan lamari da ya faru a unguwar Bolari, cikin birnin Gombe, inda wani yaron shago ya kashe...

Most Popular