HomeLabarai’Yan bindiga Sun Kashe Wata Mata Tare Da Sace Mutane 3 A...

’Yan bindiga Sun Kashe Wata Mata Tare Da Sace Mutane 3 A Kano

-

Wasu ’yanbindiga dauke da makamai sun kai hari a kauyen Yankamaye da ke cikin Karamar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano, inda suka kashe wata mata tare da sace wasu mutane uku.

 

DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar Asabar, lokacin da mazauna kauyen suka riga suka kwanta.

 

Majiyoyi a yankin sun shaida wa jaridar nan cewa ’yanbindigar sun ajiye babur-babur ɗinsu a wajen garin sannan suka shigo a kafa domin guje wa an gano su.

 

A cewar majiyoyin, ’yan bindigar sun harbe wata tsohuwa har lahira saboda ta roƙe su kada su tafi da ɗanta.

 

“Sun kashe tsohuwar ne saboda ta roƙe su kada su tafi da ɗanta. Sai suka harbe ta suka tafi da ɗan nata.

 

“Daga nan kuma suka shiga wani gida suka sace mata biyu, ciki har da surukar kansilan yankin,” in ji wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa.

 

Rundunar ’Yansanda ba ta fitar da sanarwa kan lamarin ba tukuna.

 

Kauyen Yankamaye, wanda ke kimanin kilomita 5 daga garin Rimaye a Jihar Katsina, na fama da hare-haren ’yan bindiga tun bayan da wasu al’ummomin Katsina suka rattaba hannu kan yarjejeniyar “sulhu” da su.

 

Kauyuka makwabtaka kamar Sundu da Buresawa suma na fama da irin wadannan hare-hare a kwanakin baya-bayan nan.

 

A kalla mutane takwas aka sace a wani hari da aka kai Biresawa da daddare a ranar Litinin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

FG Denies ADC Use of Eagle Square for Abuja Convention

The African Democratic Congress (ADC) has said it was denied access to both Eagle Square and the Moshood Abiola National Stadium for its planned national...

Albaba Announces Return Bid for Katsina Assembly Seat

Hon. Aliyu Albaba has declared his intention to contest for a seat in the Katsina State House of Assembly to represent Katsina Local Government Area...

Most Popular