An gudanar da babban tattakin wayar da kai kan kare hakkin dan Adam a Katsina, a ranar yancin kai ta Duniya (Human Rights Day) wanda ya gudana daga Ofishin Magajin Gari zuwa Ofishin Hukumar Kare Haƙin Ɗan Adam, dake a Unguwar Tayoyi, tare da halartar mambobin kungiyoyin kare hakki da matasa da dama a jihar.
Cibiyar International Human Rights Advocacy and Awareness Center (IHRAAC), wacce ta shirya taron, ta ce tattakin na bana ya mayar da hankali kan bukatar jama’a su daina yin shiru kan cin zarafi, musamman fyade, safarar mutane da barace-baracen yara.
Daraktan cibiyar, Dr Salisu Musa, ya ce tattakin ya nuna yadda ake bukatar karin wayar da kai a Arewacin Najeriya, yana mai cewa an dade ana boye cin zarafi saboda tsoro, al’ada ko rashin sani.
“Jama’a su sani cewa ayyukanmu kyauta ne; muna taimakawa wadanda abin ya shafa ba tare da wani kudin shiga ba, musamman wajen samun likitoci da shawarwari,” in ji Dr Musa.
Ya bukaci mata, yara da sauran al’umma da su rinka kai rahoto cikin lokaci idan aka take musu hakki, yana mai jaddada cewa kare hakkin mutum haƙƙi ne na kowa, ba na cibiyoyi kadai ba.
Tattakin na bana ya kare cikin lumana, inda mahalarta suka yi kira ga gwamnati da hukumomi su kara kaimi wajen kare marasa galihu da wadanda ake zalunta a yankunan karkara da birane.
