HomeSashen HausaMangal Ya Ɗauki Nauyin Aikin Cire Ƙaba Ga Mutane 800 a Katsina

Mangal Ya Ɗauki Nauyin Aikin Cire Ƙaba Ga Mutane 800 a Katsina

-

Gidauniyar hamshakin dan kasuwar nan Alhaji Dahiru Barau Mangal wato Mangal Foundation, ta fara gudanar da tiyatar kaba da ake kira Hernia da Hydrocele kyauta ga mutane sama da 800 a jihar Katsina.

 

An fara gudanar da aikin ne a Babbar Asibitin Katsina (General Hospital Katsina) ranar Juma’a 12 ga watan Disamba, 2025, bayan an tantance masu fama da ciwon kwanakin baya da suka wuce.

 

A lokacin tantancewan, a samu mutane a kalla 800 wa’inda suke bukatan aiki (Surgery), inda gidauniyar ta dauki nauyin masu aiki kyauta ba tare da sun biya ko naira ba.

 

Da yake magana a lokacin gudanar da aikin, ɗaya daga cikin yan kwamitin amintattu na gidauniyar, Alhaji Husssini Kabir, yace za a ci gaba da gudanar da aikin har zuwa ranar Lahadi.

 

Haka zaliki yace, bayan anyi masu aikin, gidauniyar zata dauki nauyin kula dasu har sai an sallame su daga asibiti.

 

Ya kara da cewa, “A yayin da ake gudanar da tantancewar, an duba daruruwan masu fama da laruran, inda da yawan su aka basu magunguna kyauta aka kuma sallame su.”

 

Alhaji Kabir ya shaida cewa wanna bashi bane karo na farko da ake ma masu bukata aiki kyauta, ya kara da cewa a duk shekera, ko wane zango ana gudanar da aikin.

 

Ya kuma kara jaddada cewa wanna aikin kyautane gidauniyar ke ɗaukar nauyinsa tun daga matakin sanarwa har zuwa tantancewa da kuma yin aikin tare da bada magani

 

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da wanna shirin sunyi godiya da fatan alkhairi ga shugaban gidauniyar Alhaji Ɗahiru Barau Mangal.

 

Sun kuma yi kira ga gwamnatoci, kamfanoni, da kuma masu hali da suyi koyi da Mangal wajen daukan nauyin masu karamin karfi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Nijeriya Ta Musanta Zargin Leken Asiri Kan Jirginta Da Ke Burkina-Faso

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta karyata jita-jitar da ke cewa jirginta kirar C-130 da ya sauka ba tare da shiri ba a Bobo-Dioulasso,...

Duniya Za Ta Fuskanci Ƙalubale, Idan Najeriya Ta Wargaje– Inji Sanata Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa a Najeriya, Kashim Shettima ya ce gwamnatin Tinubu ba za ta taɓa bari Najeriya ta ruguje a hannunta ba, komai rintsi.   Kamar yadda...

Most Popular