Ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin zamani, Bosun Tijani, ya ce ‘yan bindiga na amfani da “wani irin fasaha ta musamman” wajen yin kira da kuma kauce wa sa-ido daga hukumomin tsaro.
Ministan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da Seun Okinbaloye a shirin Politics Today na tashar Channels TV a daren Juma’a.
Tijani ya ce sa-ido kan kiran wayoyin ‘yan bindiga domin tattara bayanan leƙen asiri ya fi “na fasaha” fiye da yadda yawancin ‘yan Najeriya ke zato.
Ya ce masu laifin kan tura kiran waya daga hasumiya zuwa wata da dama domin rikitar da jami’an tsaro da ke bibiyar hanyoyin sadarwarsu.
“Dalilin da ya sa shugaban ƙasa ya matsa lamba mu zuba jari a hasumiyoyin sadarwa a waɗancan yankuna shi ne mun gano cewa akwai wata fasaha ta musamman da su [‘yan bindiga] ke amfani da ita wajen yin kira,” in ji Tijani.
“Ba sa amfani da hasumiyoyin sadarwa na yau da kullum; suna amfani da kira daga hasumiya zuwa hasumiya da dama. Shi ya sa suke jin daɗin zama a yankunan da ba su da haɗin sadarwa.”
Tijani ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya na aiki kan inganta tauraron dan adam (satellites) na ƙasar da ke sararin samaniya domin ƙarfafa sa-idon tsaro.
“Domin idan hasumiyoyinmu ba sa aiki, tauraron dan adam ɗinmu zai yi aiki,” in ji shi.
Ministan ya ce wannan hali ya nuna buƙatar “zuba jari mai yawa” a harkar sadarwa.
“Idan ka je ƙasar China, suna da sama da hasumiyoyin 5G miliyan huɗu. Jimillar hasumiyoyin da muke da su a Najeriya ba su wuce kusan 40,000 ba,” in ji Tijani.
