HomeLabarai'Yan'ta'adda Za Su Ɗandana Kuɗar Su Kan Harin Bom a masallacin Jihar...

‘Yan’ta’adda Za Su Ɗandana Kuɗar Su Kan Harin Bom a masallacin Jihar Borno– Inji Shettima

-

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi Allah-wadai da harin bam da ya afku a wani masallaci da ke kasuwar Gamboru a Maiduguri, Jihar Borno, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu da dama.

 

Shettima ya bayyana cewa waɗanda suka aikata harin ba za su tsira ba, inda ya tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ƙara tsaurara matakan tsaro a jihar bayan faruwar lamarin.

 

A wata sanarwa da ya fitar, Mataimakin Shugaban kasar ya ce gwamnatin tarayya na tura ƙarin jami’an tsaro na musamman domin bin sawu da kama masu hannu a harin, yana mai cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron ƙasa ba.

 

Ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Borno da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, tare da jaddada cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da bai wa hukumomin tsaro cikakken goyon baya domin murkushe ta’addanci, musamman a yankin Arewa maso gabas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Katsina Police Foil Kidnap Attempt, Rescue 18-Year-Old Girl in Danmusa LG

The Katsina State Police Command has foiled a kidnapping attempt and rescued an 18-year-old girl in Danmusa Local Government Area following a swift response by...

Harin Sojin Sama a Zamfara Ya Hallaka Sama da Mutane 100

A cikin wata sanarwa da rundunar Operation Fansan Yamma ta fitar, ta ce an kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna...

Most Popular