Majalisar Wakilai ta bayar da umarnin sake duba sabbin dokokin gyaran haraji da aka amince da su kwanan nan, biyo bayan zargin bambance-bambance tsakanin dokokin da majalisar ƙasa ta amince da su da kuma waɗanda aka wallafa bayan shugaban ƙasa ya sanya hannu.
Kakakin Majalisar, Akin Rotimi, ya ce matakin ya zama dole domin kare mutuncin majalisa, tabbatar da bin ƙa’idoji, da dawo da amincewar jama’a ga tsarin yin dokoki.
Ya bayyana cewa duk wani bambanci tsakanin kudurin doka da aka amince da shi da waɗanda aka wallafa na tauye dimokuraɗiyya da manufar dokoki.
Majalisar ta jaddada cewa dokokin haraji, saboda tasirinsu ga tattalin arziƙi, dole ne su kasance a bayyane, daidai, kuma bisa tsarin kundin mulki.
Ta kuma tabbatar da cewa za ta yi aiki da hukumomin zartarwa domin gyara matsalar tare da hana sake faruwarta, tana mai jaddada goyon baya ga gyare-gyaren da ke ƙarfafa tattalin arziƙi matuƙar an bi ka’idojin doka.
