A cewar rahoton da kafar yaɗa labarai ta ƙasar ta Fitar ta ce jirgin na dauke da makamai Masu linzami masu jagora na dabarun soja.
Wannan ci gaba na iya zama babban babbar wajen karfafa karfin rundunar sojin ruwan Pyongyang.
Sakamakon matukar wahalar fasahar da ake bukata wajen irin wannan aiki, ba a kawar da yiwuwar samun taimako daga Rasha ba.
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya kai ziyara wurin gina sabon jirgin ruwan Mai dauke da nukiliya, inda ya duba ci gaban wasu makaman karkashin ruwa na sirri.
An kiyasta nauyin jirgin ruwan ya kai kusan tan 8,700, kuma yana dauke da makamai masu linzami masu jagora na dabarun soja.
A cewar bayanin da aka fitar, “Aikin zai kara habaka karfin nukiliyar kasar da kuma kare iyakokinta a teku.”
