HomeLabaraiKotu Ta Tsare Shugaban KANSIEC da Wasu Mutum 2 Kan Zargin Badaƙalar...

Kotu Ta Tsare Shugaban KANSIEC da Wasu Mutum 2 Kan Zargin Badaƙalar Kuɗaɗe

-

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC), Sani Malumfashi, tare da Sakataren hukumar, Anas Muhammed Mustapha, da Ado Garba, Mataimakin Darakta, bisa zargin aikata badakalar kuɗi da ta kai Naira biliyan ɗaya.

‎Mai shari’a James Omotosho ne ya bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali na Kuje, Abuja, bayan da waɗanda ake tuhumar suka musanta laifuka guda shida da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta tuhume su da aikatawa.

‎A cewar ICPC, ana zargin jami’an da karɓar kuɗaɗe har Naira miliyan 450, Naira miliyan 310 da kuma Naira miliyan 260 ba bisa ƙa’ida ba, a tsakanin watan Nuwamba da Disamba na shekarar 2024, kuɗaɗen da aka ce sun sabawa doka.

‎Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Janairu, domin duba buƙatar belin waɗanda ake tuhuma, yayin da ake ci gaba da bincike kan zargin da ake musu.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, ‎lamarin dai ya ja hankalin jama’a, musamman ganin muhimmancin hukumar KANSIEC a tsarin dimokuraɗiyya da gudanar da sahihin zaɓe a Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Katsina Police Foil Kidnap Attempt, Rescue 18-Year-Old Girl in Danmusa LG

The Katsina State Police Command has foiled a kidnapping attempt and rescued an 18-year-old girl in Danmusa Local Government Area following a swift response by...

Harin Sojin Sama a Zamfara Ya Hallaka Sama da Mutane 100

A cikin wata sanarwa da rundunar Operation Fansan Yamma ta fitar, ta ce an kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna...

Most Popular