HomeSashen Hausa‎Kim Jong Un Ya Zaɓi Ƴarsa Mai Shekara 13 a Matsayin Wadda...

‎Kim Jong Un Ya Zaɓi Ƴarsa Mai Shekara 13 a Matsayin Wadda Za Ta Gaje Shi ‎

-

Rahotanni daga National Intelligence Service (NIS) sun bayyana cewa shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya zaɓi ƴarsa mai shekara 13, Kim Ju Ae, a matsayin wadda za ta gaje shi a mulki nan gaba.

Hukumar leken asirin ta sanar da ƴan majalisar dokokin Koriya ta Kudu cewa ta cimma wannan matsaya ne bayan nazarin alamu da dama, ciki har da yadda Ju Ae ke yawaita bayyana tare da mahaifinta a manyan tarukan gwamnati da muhimman al’amuran ƙasa.

‎JuJu Ae ita ce kaɗai ƴar da aka taɓa gabatarwa a fili daga cikin yaƴan Kim Jong Un da matarsa, Ri Sol Ju. Duk da haka, jami’an leken asiri na zargin cewa shugaban na da ɗa namiji wanda ba a taɓa bayyana shi a bainar jama’a ba.

A watannin baya-bayan nan, an ga Ju Ae na halartar bukukuwan soja, gwaje-gwajen makamai masu linzami da sauran muhimman taruka tare da mahaifinta—abin da masana ke ganin wata alama ce ta shirya ta domin karɓar jagoranci a nan gaba.

Rahoton jaridar Daily Trust ya tuna cewa tun bayan kafuwar ƙasar, mulki a Koriya ta Arewa ya kasance a hannun zuriyar iyalan Kim tsawon ƙarni uku—tun daga kakansa, mahaifinsa, har zuwa shi kansa.

Sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Koriya ta Arewa da ke tabbatar da batun zaɓen Ju Ae a matsayin magajiya, lamarin da ke ci gaba da janyo muhawara a tsakanin masana harkokin siyasar yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎An Cafke Wani Mutum Da Zargin Sayar Da Jaririn ‘Yar’ uwarsa Naira Miliyan 2 a Legas

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani mutum mai shekaru 30 da haihuwa bisa zargin sayar da jaririn ‘yar uwarsa mai wata daya kacal...

An Damƙa Walida Ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Namadi Ɗanmoɗi

An Damƙa Walida Ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Namadi Ɗanmoɗi Hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun damƙa matashiya Walida Abdullahi Ibrahim ga Gwamnan Jihar Jigawa,...

Most Popular