HomeSashen HausaMatashiya 'Yar Shekara 18 Daga Katsina, Ta Haddace Al-qur'ani Maigirma ‎

Matashiya ‘Yar Shekara 18 Daga Katsina, Ta Haddace Al-qur’ani Maigirma ‎

-

Wata matashiya mai suna Amina Usman, ƴar shekara 18 daga Jihar Katsina, ta samu nasarar Saukar Alƙur’ani Mai Girma a shekarar da ta gabata.

A jiya, 15 ga watan Fabrairu, 2026, aka gudanar da bikin murnar kammala hardar hizifi 40, inda iyaye, ƴan uwa da abokan arziki suka taru domin taya ta farin ciki bisa wannan babbar nasara.

Rahotannin da Nigerian Post ta samu, sun nuna cewa, Amina ta nuna jajircewa da ƙwazo tun tana ƙarama wajen karatun Alƙur’ani, lamarin da ya kai ta ga cimma wannan matsayi, Malamanta sun yaba da himmarta da ladabinta, suna mai cewa ta kasance ɗaliba mai natsuwa da kishin ilimi.

Iyaye da ƴan uwanta sun bayyana tsananin farin ciki da alfahari, tare da yi mata addu’ar Allah Ya sanya abin da ta haddace ya zama alheri a gare ta, Ya kuma yi wa karatun nata albarka, Sun ce wannan nasara ta zama abin koyi ga sauran matasa, musamman ƴan mata, wajen jajircewa kan neman ilimin addini.

Amina ta gode wa iyayenta da malamanta bisa goyon baya da kulawar da suka ba ta, tana mai jaddada aniyarta ta ci gaba da zurfafa karatu domin ƙara inganta iliminta na addini.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎An Cafke Wani Mutum Da Zargin Sayar Da Jaririn ‘Yar’ uwarsa Naira Miliyan 2 a Legas

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani mutum mai shekaru 30 da haihuwa bisa zargin sayar da jaririn ‘yar uwarsa mai wata daya kacal...

An Damƙa Walida Ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Namadi Ɗanmoɗi

An Damƙa Walida Ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Namadi Ɗanmoɗi Hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun damƙa matashiya Walida Abdullahi Ibrahim ga Gwamnan Jihar Jigawa,...

Most Popular