HomeSashen Hausa‎Majalisar Wakilai Ta Umarci A Yi Gyare-gyare a Kundin Sabbin Dokokin Haraji...

‎Majalisar Wakilai Ta Umarci A Yi Gyare-gyare a Kundin Sabbin Dokokin Haraji Bayan Samun Kura-kurai

-

Majalisar Wakilai ta bayar da umarnin sake duba sabbin dokokin gyaran haraji da aka amince da su kwanan nan, biyo bayan zargin bambance-bambance tsakanin dokokin da majalisar ƙasa ta amince da su da kuma waɗanda aka wallafa bayan shugaban ƙasa ya sanya hannu.

‎Kakakin Majalisar, Akin Rotimi, ya ce matakin ya zama dole domin kare mutuncin majalisa, tabbatar da bin ƙa’idoji, da dawo da amincewar jama’a ga tsarin yin dokoki.

‎Ya bayyana cewa duk wani bambanci tsakanin kudurin doka da aka amince da shi da waɗanda aka wallafa na tauye dimokuraɗiyya da manufar dokoki.

‎Majalisar ta jaddada cewa dokokin haraji, saboda tasirinsu ga tattalin arziƙi, dole ne su kasance a bayyane, daidai, kuma bisa tsarin kundin mulki.

‎Ta kuma tabbatar da cewa za ta yi aiki da hukumomin zartarwa domin gyara matsalar tare da hana sake faruwarta, tana mai jaddada goyon baya ga gyare-gyaren da ke ƙarfafa tattalin arziƙi matuƙar an bi ka’idojin doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎Kwankwaso Ya Bayyana Wadanda Zasu Yi Takarar Zaben Cike Gurbi A Jam’iyyar NNPP

Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya amince da bai wa ’ya’yan ’yan Majalisar Jiha biyu da suka rasu, damar tsayawa takara, domin neman...

‎Gwamnatin Tarayya ta Kammala Horas da Sama da Jami’an Tsaron Daji 7,000 a Jihohi 7

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce ta kammala horas da sama da sabbin jami’an tsaron daji 7,000 da aka dauka aiki daga jihohi bakwai, a wani...

Most Popular