HomeSashen Hausa‎Kwankwaso Ya Bayyana Wadanda Zasu Yi Takarar Zaben Cike Gurbi A Jam'iyyar...

‎Kwankwaso Ya Bayyana Wadanda Zasu Yi Takarar Zaben Cike Gurbi A Jam’iyyar NNPP

-

Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya amince da bai wa ’ya’yan ’yan Majalisar Jiha biyu da suka rasu, damar tsayawa takara, domin neman cike guraben kujerun iyayensu a Majalisar Dokokin Jihar ta Kano.

‎Matakin wanda ya shafi kujerun wakilcin Ungogo da Birnin Kano, inda ’ya’yan kowane daya daga cikin ’yan majalisar za su fafata a zaben cike gurbin kujerun karkashin tutar jam’iyyar NNPP.

‎Majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa wannan mataki na daga cikin kokarin NNPP na tabbatar da ci gaba da wakilci da kuma girmama gudunmawar da ’yan majalisar suka bayar wajen hidimar al’ummar yankunansu a lokacin da suke raye.

‎Ana sa ran wannan mataki zai jawo ra’ayoyi mabanbanta a fagen siyasar Jihar Kano, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zabukan cike gurbin kujerun da ke tafe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Abinda Ya Faru Da Ni Ya Zame Min Alkhairi– Malam Bala Dorayi

Malam Bala Dorayi, wanda aka fi sani da Sarkin Yakin Karyar Ƙasar Hausa, ya bayyana cewa abin da ya faru da shi a baya kaddara...

‎Kim Jong Un Ya Zaɓi Ƴarsa Mai Shekara 13 a Matsayin Wadda Za Ta Gaje Shi ‎

Rahotanni daga National Intelligence Service (NIS) sun bayyana cewa shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya zaɓi ƴarsa mai shekara 13, Kim Ju Ae,...

Most Popular