Rundunar ‘yansanda a jihar Kebbi ta tabbatar da afkuwar fashewar bam da sanyin safiyar Talata a babban asibitin Bagudo, da ke karamar hukumar Bagudo ta jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Bashir Usman, ya fitar a Birnin Kebbi.
Usman ya ce: “Muna son tabbatar wa mazauna yankin cewa an shawo kan al’amuran tsaro gaba ɗaya bayan wata babbar kara ta fashewa da ta auku a babban asibitin Bagudo da sanyin safiyar Talata, 30 ga Disamba.
“Ƙungiyar tsaro ta haɗin gwiwa wadda ta ƙunshi ‘yansanda, sojoji da ‘yan sa-kai ta kulle tare da tabbatar da tsaron yankin cikin gaggawa. Ƙwararrun jami’an EOD-CBRN suna wurin suna gudanar da cikakken bincike.
“Muna farin cikin sanar da cewa babu wanda ya rasa ransa. Duk da cewa wani gini a bangaren ma’aikata ya lalace, mazauna wajen sun riga sun fice lafiya.
“Kwamishinan ‘yansanda na jihar ya ƙara tura jami’an tsaro na musamman domin tabbatar da zaman lafiya da doka.”
