Rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF), a karkashin rundunar FANSAN YANMA, ta samu babban nasara a jihar Katsina bayan kai farmaki na sama da ya hallaka wasu ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Faskari
Zagazola ya samu labarin cewa an gudanar da farmakin ne a safiyar 1 ga watan Fabrairu, inda aka kai hari kan sansanonin da ake zargin ‘yan bindiga suna taruwa a dajin Shawu–Mununu Ruwan Godiya a yankin faskari.
Majiyoyi sun ce farmakin ya biyo bayan dogon bincike na sama da ya tabbatar da kasancewar ‘yanbindiga masu makamai a yankin Bakori–Guga, waɗanda ake zargi da kai hare-hare kwanan nan.
An yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga hukumomi domin taimaka musu wajen gano motsin ‘yan ta’adda.
