HomeLabaraiAbinda Ya Faru Da Ni Ya Zame Min Alkhairi– Malam Bala Dorayi

Abinda Ya Faru Da Ni Ya Zame Min Alkhairi– Malam Bala Dorayi

-

Malam Bala Dorayi, wanda aka fi sani da Sarkin Yakin Karyar Ƙasar Hausa, ya bayyana cewa abin da ya faru da shi a baya kaddara ce daga Allah, amma daga ƙarshe ya zame masa alkhairi.

Malam Bala Dorayi ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce duk da ƙalubalen da ya fuskanta, lamarin ya buɗe masa sabbin ƙofofi na alheri da bai taɓa tsammani ba.

‎Abin da ya same ni kaddara ce. A farko na ɗauka wata jarabawa ce mai tsauri, amma daga baya na ga cewa alkhairi ne Allah Ya ɓoye a cikinsa, in ji shi.

Ya ƙara da cewa a halin yanzu yana samun tallafi da goyon baya daga jama’a da dama, ciki har da addu’o’i da fatan alkhairi, wanda ya ce hakan na ƙara masa ƙarfin gwiwa da kwarin guiwa.

Har ila yau, ya gode wa dukkan waɗanda suka tsaya masa a lokacin ƙalubalen, yana mai jaddada cewa zai ci gaba da jajircewa wajen gudanar da harkokinsa cikin gaskiya da riƙon amana.

Rahotanni na nuni da cewa kalaman nasa sun ja hankalin mabiyansa da dama, inda suka bayyana farin cikinsu kan yadda lamarin ya juya zuwa alheri a rayuwarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Katsina Police Foil Kidnap Attempt, Rescue 18-Year-Old Girl in Danmusa LG

The Katsina State Police Command has foiled a kidnapping attempt and rescued an 18-year-old girl in Danmusa Local Government Area following a swift response by...

Harin Sojin Sama a Zamfara Ya Hallaka Sama da Mutane 100

A cikin wata sanarwa da rundunar Operation Fansan Yamma ta fitar, ta ce an kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna...

Most Popular