HomeLabaraiHisbah Ta Kama Ma’aurata Kan Zargin Bada Aron Matansu A Bauchi

Hisbah Ta Kama Ma’aurata Kan Zargin Bada Aron Matansu A Bauchi

-

Hukumar Hisbah a shiyyar Katagum, da ke garin Azare ta Jihar Bauchi, ta ce ta kama wasu matasa ma’aurata bisa zargin aikata wani abu da ya sabawa addini da al’ada, wato musayar matan su na aure ga Abokansu a tsakaninsu.

A rahoton da Nigerian Post ta bibiya, Kwamandan Hisbah na yankin, Malam Rilwanu Kairan, ya shaida wa Manema Labarai cewa lamarin ya faru ne a ranar da aka kama mutanen, bayan samun bayanai kan abin da ke faruwa.

Ya ce abin ya ba su matuƙar takaici, yana mai cewa mutanen da aka kama sun amsa zargin da ake musu, tare da bayyana cewa sun ɗauki abin a matsayin wata akida da suka amince da ita.

A cewar kwamandan, hukumarsu ba za ta lamunci irin wannan ɗabi’a ba, domin ta ci karo da koyarwar addinin Musulunci da kuma al’adun Hausawa.

A nasa ɓangaren, wani babban malami da ake dangantawa da mutanen, ya musanta cewa abin yana da alaƙa da wata koyarwa ta addini ko wata darika, yana mai cewa sun yi watsi da irin wannan hali.

Hukumar Hisbah dai ta ce tana ci gaba da bincike kan lamarin domin ɗaukar matakin da ya dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‘Yanbindiga Sun Sace Mutane 15 a Bakori, Jihar Katsina

Rahotanni daga jihar Katsina sun tabbatar da cewa wasu ’yan bindiga sun kai hari a unguwar Sabon Layi da ke gundumar Kakumi, a karamar hukumar...

KASEDA Trains 60 Youths on Business Growth in Katsina

Sixty young men and women who benefited from a business development training programme in Katsina have commended Governor Radda and the management of KASEDA for...

Most Popular