Tuesday, June 16, 2026
HomeLabaraiKotu Ta Yanke Wa Wata Mai Safarar Alburusai Hukuncin Kisa Ta Hanyar...

Kotu Ta Yanke Wa Wata Mai Safarar Alburusai Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya a Katsina

‎Wata Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Katsina ta yanke wa wata mata mai suna Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifin haɗa baki wajen aikata ta’addanci da kuma taimakawa ayyukan ta’addanci.

‎Rahotanni sun nuna cewa jami’an Department of State Services (DSS) sun kama Hauwa’u Mukhtar a ranar 16 ga watan Satumbar 2023 a tashar mota ta Jibia da ke jihar Katsina, yayin da ake zarginta da ƙoƙarin kai harsasai guda 438 na bindigar 7.62mm ga wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga mai suna Ado, wanda ke gudanar da ayyukansa a dajin Dunburum da ke jihar Zamfara.

‎A cewar masu gabatar da ƙara, an tabbatar wa kotu cewa wadda ake tuhuma ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da kayan aiki ga ƙungiyoyin masu aikata ta’addanci, lamarin da kotun ta ce ya zama barazana ga tsaron ƙasa.

‎Hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro ke ci gaba da matsa kaimi wajen dakile hanyoyin safarar makamai da alburusai zuwa hannun ‘yanbindiga da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka a sassan arewa maso yammacin Najeriya.

‎Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin DSS ba su fitar da ƙarin bayani kan ko wadda aka yanke wa hukuncin za ta daukaka ƙara ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments