HomeSashen HausaNUPSRAW Ta Yabawa Gwamna Radda Akan Biyan Albashin Ma'aikata Kan Kari

NUPSRAW Ta Yabawa Gwamna Radda Akan Biyan Albashin Ma’aikata Kan Kari

-

Kungiyar Sakatarori Da Masu Fitarwa Da Adana Bayanai Ta Kasa Reshen Arewacin Najeriya(NUPSRAW),ta yabawa Gwamna Dikko Ummaru Radda akan yadda yake biyan albashin ma’aikata akan kari.

Manyan jami’an Kungiyar ne suka yi wannan yabo a lokacin taron Kungiyar na Arewacin Najeriya da ya gudana a Jihar Katsina.

Da yake gabatar da jawabi,Gwamna Dikko Radda wanda mai taimaka mashi akan Kwadago Kwamarad Tanimu Saulawa ya wakilta,ya yabawa ya’yan Kungiyar akan gudummuwar su ga samun nasarar Gwamnatin shi.

Gwamna Dikko Radda wanda ya bayyana aikin ya’yan Kungiyar a matsayin mai matukar muhimmanci, ya magantu akan dumbin ayyukan raya kasa da cigaban al’umma da Gwamnatin shi ta shimfida a Jihar.

Daga nan sai ya bukaci karin hadin kai da fahimtar juna a tsakanin ya’yan Kungiyar domin su cimma karin nasarori.

Shugaban Ma’aikata na Jihar Katsina Alhaji Falalu Bawale,wanda Daraktan Kudi na Ofishin shi ya wakilta,ya yabawa Kungiyar ta NUPSRAW akan zaben Jihar Katsina domin gudanar da zaben.

A jawaban su daban-daban,Tsohon Shugaban Kungiyar na Kasa Kwamarad Y.Y Yashi da Shugaban Zauren Tuntuba na Arewacin Najeriya kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Kasafin Kudi ta Jihar Zamfara,sun yabawa Gwamna Dikko Radda akan yadda yake kula da cigaban ma’aikata a Jihar Katsina.

Sun nanata kudirin su na cigaba da yin bakin kokari ta fuskar kawo cigaban Kungiyar,domin a gudu tare a tsira tare.

Shugaban Kungiyar ta NUPSRAW na Jihar Katsina Kwamarad Muhammad Halliru,ya ce sun gamsu da tafiyar gwamnatin Malam Dikko RaÉ—É—a ganin yadda ta ke tsare hakkokin ma’aikata.

Ya kuma yabawa gwamnatin bi sa yadda take basu gudunmawa da goyan baya a duk lokacin da suka je mata da wata buƙata.

Sauran Wadanda suka maganta sun hada da Shugaban Kungiyar Kwadago na Jihar Katsina Kwamarad Hussaini Yanduna,wanda Shugaban Kungiyar RATTAWU Kwamarad Buhari Rafukka ya wakilta,sai wakilin Ma’aikatar Kwadago da Ingantuwar Ayyuka da sauran su.

Taron ya samu halartar ya’yan Kungiyar daga dukkan Jihohin Arewacin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Jirgin Rano Air Ya Samu Matsalar Injin Saman Iska Kan Hanyar Sa Ta Zuwa Katsina

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta bayar da umarnin tsayar da wani jirgin sama na kamfanin Rano Air mai lamba 5N-BZY,...

Nasarori 12 Da Dakta Abdullahi Umar Ganduje Ya Kafa A Shugabancin APC

Jerin basarori 12 da Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kafa a shugabancin jam'iyyar APC na ƙasa da babu shugabanta da ya taɓa kafawa a cikin...

Most Popular