Za a Dinga Koyar Da Yaren Chana A Makaratun Sakandare Na Najeriya- Gwamnatin Taraiya
Gwamnatin Tarayya ta sanar da saka harshen Chana (Mandarin) a cikin kundin karatun makarantun sakandare a Najeriya.
Sakataren Ilimi na Abuja, Dakta Danlami Hayyo ne ya bayyana hakan a Abuja yayin kaddamar da “Chinese Corner” na 14, inda ya ce wannan mataki na nuna muhimmancin harshen Mandarin a kasuwanci, ilimi, al’adu da diflomasiyya.
Ya ce koyar da ɗalibai harshen zai ba su damar gogayya a duniya tare da samun damar ilimi da kasuwanci.
A cewarsa, wannan shiri wani bangare ne na ƙoƙarin gwamnati wajen shirya matasa domin zama masu iya yin gogayya a fagen duniya.
Ana ganin matakin zai kara zurfafa dangantakar Najeriya da ƙasar China a fannoni da dama, musamman ilimi da musayar al’adu.