HomeSashen HausaGwamnatin Taraiya Ta Bada Umarnin A Riƙa Rera Baitin Farko Kaɗai Na...

Gwamnatin Taraiya Ta Bada Umarnin A Riƙa Rera Baitin Farko Kaɗai Na Taken Nijeriya A Wajen Taruka

-

Hukumar Wayar da kan Ƴan ƙasa (NOA) ta fitar da sabbin ka’idoji game da yadda za a rera taken ƙasar Najeriya.

 

An fitar da wannan umarni mai ɗauke da bayanai huɗu ne a cikin wata sanarwa da aka saki a ranar Alhamis.

 

Sanarwar ta ce: “A rera ko a karanta baitin farko kawai (ba duka baitoci uku ba) a dukkan tarukan gwamnati.”

 

“Haka kuma baitin na uku shi ne za a karanta a matsayin Addu’ar Ƙasa a farkon kowane taro.”

 

“Dukkan baitoci uku na taken ƙasa za a rera su ne kawai a lokutan musamman kamar Ranar ‘Yancin Kai da Ranar Rantsar Shugaban Ƙasa da Ranar Tunawa da Sojoji da Ranar Dimokuraɗiyya (12 ga Yuni), da Ranar Rantsar da Majalisar Dokoki ta Ƙasa, da sauransu.”

 

A watan Mayun da ya gabata, Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan kudirin da ya dawo da tsohon taken ƙasa mai taken ‘Nigeria, We Hail Thee’.

 

Wannan taken ya maye gurbin tsohon da aka rika rerawa tun daga shekarar 1978 mai taken ‘Arise, O Compatriots’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Dalilan Da Ya Sa Na Bar APC Na Koma ADC– Inji Wada Protocol

‎Tsohon hadimin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, Alhaji Mustapha Abdu Saulawa, wanda aka fi sani da Wada Protocol, ya bayyana dalilin da...

Yaron Shago Ya Hallaka Ubangidansa da Almakashi a Gombe, Kwanaki Kadan Da Aurensa

Jihar Gombe ta shiga alhini biyo bayan wani mummunan lamari da ya faru a unguwar Bolari, cikin birnin Gombe, inda wani yaron shago ya kashe...

Most Popular