HomeSashen HausaAn ci tarar Katsina United Miliyan 9 da hana su buga wasa...

An ci tarar Katsina United Miliyan 9 da hana su buga wasa a Gida

-

Hukumar NPFL mai kula da gasar ƙwallon ƙafa ta firimiyar Najeriya ta ci tarar ƙungiyar Katsina United naira miliyan tara sakamakon hatsaniyar da magoya bayanta suka tayar ranar Asabar.

Wata sanarwa da NPFl ta fitar a yau ta ce mahukuntan Katsina United sun gaza “samar da cikakken tsaro abin da ya jawo magoya baya suka shiga cikin fili” a wasansu da Barau FC a garin na Katsina.

Magoya bayan Katsina sun auka cikin filin ne jim kaɗan bayan Barau ta farke ƙwallon da Katsina ta zira mata, inda ɗaya daga cikinsu ya ji wa ɗanwasan barau rauni a wuya.

“An ci tarar kulob ɗin naira miliyan ɗaya kan kowane laifi uku da suka haɗa da jejjefa abubuwa cikin fili, da rashin tsawatar wa magoya, da kuma haddasa hatsaniya yayin wasa,” in ji sanarwar.

“Haka kuma, Katsina za ta biya tarar miliyan biyu kan gazawa wajen samar da cikakken tsaro a filin wasa.

“Sannan za ta biya miliyan biyu kan kowane laifi biyu na ɗaukar nauyin gyaran motocin Barau FC da aka lalata, da kuma ɓata wa alƙalan wasa da ‘yan Barau FC lokaci bayan tashi daga wasan.”

Jimilla Katsina United za ta biya tarar naira miliyan tara kenan, amma NPFL ta ce tana da 48 na ɗaukaka ƙarar hukuncin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎Kim Jong Un Ya Zaɓi Ƴarsa Mai Shekara 13 a Matsayin Wadda Za Ta Gaje Shi ‎

Rahotanni daga National Intelligence Service (NIS) sun bayyana cewa shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya zaɓi ƴarsa mai shekara 13, Kim Ju Ae,...

‎’Yan Najeriya Biyu Sun Mutu a Yaƙin Ukraine

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ƴan Najeriya biyu – Hamzat Kazeem Kolawale da Mbah Stephen Udoka – sun rasu a ƙasar Ukraine yayin da suke...

Most Popular