HomeLabarai'Yansanda Sun Cafke Mai Gadi Da Abokinsa Kan Zargin Halaka Tsohuwar Mai...

‘Yansanda Sun Cafke Mai Gadi Da Abokinsa Kan Zargin Halaka Tsohuwar Mai Shari A Jihar Delta

-

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta ta tabbatar da kama mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa tsohuwar alkaliyar Babban Kotun jihar, Mai Sharia Ifeoma Okogwu (Rtd.), wadda aka tsinci gawarta a falonta, hannayen ta ƙafafu da bakin a daure cikin yanayi mai tayar da hankali.

‎Mai magana da yawun rundunar, DSP Bright Edafe, ya bayyana cewa jami’an sashen binciken kisan kai na CID sun cafke wanda ake zargi, Godwin Mngumi, wanda shi ne mai gadi a gidan marigayiyar. An kama shi ne a jihar Anambra, kuma an same shi da wayar marigayiyar, alamar da ta ƙara tabbatar da zargin da ake masa.

‎A cewar Edafe, Mngumi ya amsa laifi, inda ya bayyana cewa shi ne ya shirya kai farmakin, tare da gayyatar wasu abokansa domin su taimaka wajen aikata wannan ta’asa.

‎“Ya amsa cewa ya gayyaci abokinsa Nnaji Obalum da wani mutum na uku da ya tsere. Sun kutsa cikin gidan ne suka yi kisan tare,” in ji Edafe cikin sanarwar.


‎Binciken ya kai ga kama Nnaji Obalum, yayin da ake cigaba da neman mutum na ukun da ya gudu domin fuskantar shari’a.

‎Tun farko dai, an gano gawar tsohuwar tsohuwar Mai Shari’arne a ranar 6 ga watan Disamba a gidanta da ke Asaba. Inda rahotanni suka tabbatar da cewa an sami alamun turjiya da cin zarafi a wajen, abin da ya tayar da hankalin mazauna unguwar da al’ummar jihar baki ɗaya.

‎Rundunar ’yan sandan ta ce tana ci gaba da zurfafa bincike don tabbatar da cewa duk masu hannu a wannan aika-aika sun fuskanci hukunci yadda doka ta tanada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Katsina Police Foil Kidnap Attempt, Rescue 18-Year-Old Girl in Danmusa LG

The Katsina State Police Command has foiled a kidnapping attempt and rescued an 18-year-old girl in Danmusa Local Government Area following a swift response by...

Harin Sojin Sama a Zamfara Ya Hallaka Sama da Mutane 100

A cikin wata sanarwa da rundunar Operation Fansan Yamma ta fitar, ta ce an kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna...

Most Popular