HomeSashen HausaOdua People’s Assembly Ta Nemi Gwamnati Ta Gudanar Da Bincike Gaggawa Kan...

Odua People’s Assembly Ta Nemi Gwamnati Ta Gudanar Da Bincike Gaggawa Kan Matawalle

-

Sun ce, zargin alaƙa da ‘yan bindiga barazana ce ga tsaron Najeriya.

 

Ƙungiyar Odua People’s Assembly (OPA) ta nuna damuwa matuƙa kan zargin da ake yi wa Ministan Tsaron Ƙasa (State), Bello Matawalle, dangane da alaƙa da ‘yan bindiga. Ƙungiyar ta ce zargin yana da hatsari ga tsaron ƙasa da amincewar jama’a.

 

OPA ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta gudanar da bincike mai zaman kansa, tare da sanya gaskiya kuma ba tare da son kai ba, domin fayyace gaskiyar lamarin. Ta ce rashin daukar mataki zai ƙara raunana amincewar jama’a da hukumomin gwamnati, musamman a lokacin da Najeriya ke fama da matsanancin matsalar tsaro.

 

Ƙungiyar ta ce bayyanar wani bidiyo da ke nuna Bello Turji, shugaban ‘yan bindiga, yana kare Matawalle abin tayar da hankali ne, domin yana nuna yiyuwar haɗin kai tsakanin jami’an gwamnati da masu laifi.

 

OPA ta bayyana cewa duk wata alaƙa, kai tsaye ko a kaikaice, tsakanin jami’an gwamnati da ‘yan bindiga cin amanar ‘yan Najeriya ne, musamman waɗanda suka sha wahala sakamakon rashin tsaro.

 

A matsayin mataki na dawo da amincewar jama’a, OPA ta buƙaci a sauke Matawalle daga muƙaminsa nan take, tare da kafa cikakken tsari na bincike mai zaman kansa. Ta kuma gargadi cewa rashin daukar mataki mai tsauri zai ƙarfafa ‘yan bindiga tare da ƙara ta’azzara rashin tsaro.

 

Ƙungiyar ta bukaci ‘yan Najeriya su kasance masu faɗakarwa, su kuma riƙa kira ga alhakin shugabanni, tana jaddada cewa yaƙi da ‘yan bindiga ya zama na bai ɗaya, ba tare da la’akari da siyasa ko yanki ba.

 

Sa Hannun;

Sunday Daniel

Mai magana da yawun Odua People’s Assembly

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Kwamishinan ’Yansanda Ya Karɓi Baƙuncin Sabon Kwamandan Rundunar Sojin Saman Najeriya Da Aka Turo Katsina

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Katsina, CP Bello Shehu, MNIM, ya karɓi bakuncin sabon Kwamandan da aka turo na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, 213...

Tsohon gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya koma jam’iyar APC

Bafarawa da magoya bayansa sun bayyana komawa jam'iyar APC a babban xakin taro na gidansa dake jihar Sakkwato a ranar Laraba.   Tsohon Gwamnan ya ce magoya...

Most Popular