HomeSashen HausaAlƙalin-alƙalai Na Katsina, Ya Gargaɗi Matasa Kan Aikata Laifuka Ta Yanar Gizo

Alƙalin-alƙalai Na Katsina, Ya Gargaɗi Matasa Kan Aikata Laifuka Ta Yanar Gizo

-

Alƙalin-alƙalai dake Katsina, Mai shari’a Musa Danladi Abubakar, ya gargaɗi Matasa a jihar da su guji shiga duk wani nau’i na aikata laifuka musamman ta yanar gizo.

Kamr yadda NAN ta rawaito, taron wanda cibiyar koyar da sana’o’in hannu ta Katsina ta ɗauki nauyin gudanar da bada horaswar, an samu ziyarar mahalarta da suka fito daga ƙananan hukumomi da dama a faɗin jihar.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Mista Danladi Abubakar ya bayyana haka a lokacin da ake yaye Matasa 75 da suka kammala horon kwanaki Uku kan yadda ake amfani da wayar hannu, ranar Laraba 10 ga watan Satumba 2025.

Ya lura da cewa, duk wata shari’ar da aka kai ta yanar gizo a kotu mai laifin ba’a iya kare shi, domin an tabbatar da laifin da hujjoji.

A cewarsa, wata sabuwar doka ta tanadi hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan yari ga duk wanda aka samu da laifin yin amfani da yanar gizo.

Ya ƙara yin gargadin cewa, dole ne Matasa su yi taka-tsan-tsan wajen amfani da kafafen sada zumunta, yana mai jaddada cewa, yin amfani da rashin bin doka zai iya sanya masu amfani da yanar gizo abin ya shafe su ba tare da sun iya kare kansu ba.

Mista Danladi-Abubakar ya bayyana horon a matsayin wata babbar dama ga waɗanda suka ci gajiyar shirin, ya kuma buƙace su da su faɗaɗa ilimin da suka samu ga al’ummarsu.

Tun da farko, shugaban cibiyar, Danjuma Mohammed, ya ce an kafa ta ne a shekarar 2001 da marigayi MD Yusuf ya kafa. Ya kuma ba da tabbacin cewa cibiyar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba a ƙoƙarinta na yin tasiri ga rayuwar Matasa a faɗin Katsina.

Malam Danjuma, ya ƙara da cewa, cibiyar tana tattaunawa da shuwagabannin ƙananan hukumomi, domin gabatar da waɗanda suka ci gajiyar shirin tare da samar da tallafi don tsawaita horon.

Ya kuma bayyana cewa, manufar shirin ita ce a baiwa Matasa da dama al’ummomi daban-daban na jihar, damar cin gajiyar ilimin ga waɗanda aka ba horon.

Wasu da suka ci gajiyar shirin sun yaba da shirin, inda suka yi alkawarin yin amfani da ilimin yadda ya kamata, tare da miƙa shi ga sauran jama’ar yankinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

SAKON ƘARSHEN SHEKARA NA KATSINA TIMES: Mun Fuskanci Barazana Da Kalubale A Shekarar 2025– Inji Malam Muhammad Danjuma Katsina

Tunda farko, ya yi godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, tare da salati da aminci ga Manzon Rahama, Annabi Muhammad (SAW), iyalansa (AS) da sahabbansa (RA),...

Obi Na Shirin Shiga ADC Yayin Da Jam’iyyar Za Ta Yi Babban Taron Ta Na Ƙasa a 2026

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party (LP), Peter Obi, na dab da shiga jam’iyyar ADC, gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Wata majiya a jam’iyyar...

Most Popular