Saturday, June 13, 2026
HomeLabaraiRundunar Sojin Sama Ta Yi Luguden Wuta Kan Maɓoyar Yanta'adda A Dajin...

Rundunar Sojin Sama Ta Yi Luguden Wuta Kan Maɓoyar Yanta’adda A Dajin Sambisa

Rundunar Sojin Sama ta Ƙasa ta ce ta ƙaddamar da luguden wuta mai ƙarfi a Arra, wani sanannen mafakar ƴan ta’adda a Sambisa.

 

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a da Bayar da Bayanai, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a jiya Laraba a Abuja.

 

Ya ce an gudanar da luguden ne bayan umarnin da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya bayar.

 

Ejodame ya ce an kai harin ne bayan bayanan sirri da sa ido da kuma bincike da suka gano motsin ‘yan ta’adda bayan kwanton ɓaunar da aka yi a Kashomri ranar 17 ga Oktoba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments