HomeSashen HausaMatashi Ya Hallaka Mata Da Jaririnta Ɗan Wata 10 A Katsina

Matashi Ya Hallaka Mata Da Jaririnta Ɗan Wata 10 A Katsina

-

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani matashi, Sahabi Rabi’u, mai shekara 35, wanda ake zargi da kashe wata mata da jaririnta ɗan wata 10 da take shayar da shi a ƙauyen Sheme da ƙaramar hukumar Faskari.

 

A wani rahoto da Nigerian Post ta samu daga Premium Times Hausa, Mai magana da yawun rundunar, Abubakar Aliyu, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis cewa Rabi’u ya amsa laifinsa na kashe matar mai shekara 30 a duniya, da ɗanta bayan haɗa baki da wani mutum wanda a yanzu ake nema ruwa a jallo.

 

A cewar rundunar ‘yan sandan, wanda ake zargin ya yaudari matar zuwa bayan garin Sheme inda ya kashe ta sannan ya jefa gawarta a wata rijiya da ke kusa da wajen.

 

Binciken ‘yan sanda ya nuna cewa dalilin kisan ya samo asali ne daga rikici tsakanin wanda ake zargi da wadda aka kashe.

 

“An samo gawar waɗanda aka kashe kuma a yanzu haka ana tsare da wanda zargin,” a cewar sanarwar. “Haka kuma ana cigaba da ƙoƙarin ganin an kama ɗayan da ake zargi wanda ya gudu.”

 

Kwamishinan ‘yan sanda Katsina, Bello Shehu, ya yi Alla-wadai da kisan, yana mai bayyana kisan da “rashin imani”. ya kuma bai wa al’umma tabbacin cewa rundunar za ta tabbatar da an yi adalci.

 

Rundunar ta nemi al’umma da su bayar da bayanai da za su taimaka wajen gano ɗaya wanda ake zargin, tana mai tabbacin ɓoye bayanan duk wanda ya ba da bayanan sirrin.

 

Kuma rundunar ta ce tana cigaba da gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Dalilan Da Ya Sa Na Bar APC Na Koma ADC– Inji Wada Protocol

‎Tsohon hadimin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, Alhaji Mustapha Abdu Saulawa, wanda aka fi sani da Wada Protocol, ya bayyana dalilin da...

Yaron Shago Ya Hallaka Ubangidansa da Almakashi a Gombe, Kwanaki Kadan Da Aurensa

Jihar Gombe ta shiga alhini biyo bayan wani mummunan lamari da ya faru a unguwar Bolari, cikin birnin Gombe, inda wani yaron shago ya kashe...

Most Popular