Sunday, June 21, 2026
HomeLabaraiBa Da Jimawa Ba Za Mu Kawo Ƙarshen Rikicin Masarautar Kano– Gwamnatin...

Ba Da Jimawa Ba Za Mu Kawo Ƙarshen Rikicin Masarautar Kano– Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce nan ba jimawa ba za ta kawo karshen rikicin da ya daɗe yana faruwa kan masarautar Kano, inda mutum biyu ke ikirarin kasancewa halastattun sarakuna.

 

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’amuran Cikin Gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ya ce gwamnati ta tsara abubuwa na musamman domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan sarautar.

 

Kusan shekaru biyu kenan Kano na fama da rikicin sarauta, inda Sarki Muhammadu Sanusi II ke zaune a fadar Gidan Rumfa, yayin da Sarki Aminu Ado Bayero ke zaune a fadar Nassarawa ƙarƙashin tsaron jami’an gwamnatin tarayya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments