Jam’iyyar ADC ta yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC na da hannu wajen ƙirƙirar sabuwar jam’iyyar NDC domin raunata haɗin kan jam’iyyun adawa kafin babban zaɓen shekarar 2027.
A cewar ADC, kafa jam’iyyar NDC wani salo ne na siyasa da ake amfani da shi wajen rage ƙarfin haɗin gwiwar ƴan adawa tare da raba kuri’un masu goyon bayan su a faɗin ƙasar nan.
Jam’iyyar ta bayyana cewa wannan mataki na iya kawo tsaiko ga yunƙurin da jam’iyyun hamayya ke yi na haɗa kai domin tunkarar APC a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
ADC ta kuma nuna cewa maimakon a ƙarfafa tsarin dimokaraɗiyya da ba kowa damar fafatawa cikin gaskiya, ana amfani da sabbin dabaru wajen rage tasirin jam’iyyun adawa a harkokin siyasar Najeriya.
Sai dai jam’iyyar APC ta nesanta kanta daga zargin, tana mai cewa babu wata alaƙa tsakaninta da kafa jam’iyyar NDC.
APC ta bayyana zargin da cewa ba shi da hujja, tare da jaddada cewa tana gudanar da siyasa bisa tsarin dimokaraɗiyya da doka.
Wannan muhawara na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ci gaba da shirye-shirye da tattaunawar kafa kawance gabanin zaɓen shekarar 2027.
