Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, ya yi alƙawarin share ma Mazauna yankunan Eka, Iyatawa da Remawa da ke ƙaramar hukumar Rimi Hawaye, bayan sun roƙi Gwamna Malam Dikko Umaru Radda da ya sake gina titin Eka–Iyatawa–Remawa, a jihar Katsina.
Mazauna waɗannan yankunan sun yi wannan kira ne a ranar Asabar yayin da Gwamna Radda ke bi ta wannan hanya zuwa Remawa domin ƙaddamar da cibiyar lafiya da Mai Shari’a ta Samar.
Tunda farko, da yake ƙaddamar da cibiyar lafiyar, Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta riga ta amince da aikin gina titin, kuma an sanya shi cikin jerin ayyukan da za a fara aiwatarwa nan ba da jimawa ba.
Haka kuma gwamnan ya yi alƙawarin faɗaɗa shirin samar da ruwan sha na karkara zuwa Iyatawa da sauran ƙauyukan da ke makwabtaka da yankin domin magance matsalar ƙarancin ruwa.
Dikko ya ce, tun daga Eka har zuwa Remawa, abin da jama’a suke nema shi ne a gina wannan hanya, inda ya roke su da su da yi haƙuri, domin an riga an saka titin daga cikin waɗanda za a gina, ya jaddada cewa, abin da ya rage kawai shi ne a fara aikin, kuma da yardar Allah za a gina shi.
Ya ƙara da cewa, ya kuma saurari koken wasu yara a Iyatawa game da rashin ruwa suna mai tabbatar ma su cewa cikin kwanaki masu zuwa za su samar da ruwan sha ga wannan al’umma.
A ƙarshe, Gwamna Radda ya yaba wa Mai Shari’a Binta Nyaku bisa gina cibiyar lafiyar, gidan ma’aikatanta da kuma tsarin hasken rana da aka samar domin amfanin al’ummar Remawa.
Ya ce suna matuƙar gode mata bisa wannan aikin alheri. Haka kuma suna kira ga duk masu hali da matsayi da su riƙa tallafa wa al’ummominsu ta hanyar aiwatar da ayyukan da za su amfanar da jama’a sosai.
