An Rufe Jama’ar UMYUK Katsina Sai Baba Ta Gani
Kungiyoyin Malamai da ma’aikatan Jami’ar Ummaru Musa Yar’adua (UMYU) a Katsina sun tsunduma yajin aiki “sai baba ta gani” a ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamba 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa, yajin aikin ya shafi dukkan Malamai da ma’aikatan jami’ar, sakamakon wasu matsalolin da suke zargin gwamnati ta yi biris da su. Daga cikin korafe-korafen da suka gabatar sun hada da; Rashin ingantaccen jin daɗin ma’aikatan jami’ar, Matsalar kwace ikon gudanar da shafin (portal) na makaranta.
Sauran sun hada da Karancin kuɗaɗen gudanarwa, da kuma batun walwalar Ɗalibai.
Sai dai a nata ɓangaren, Gwamnatin Jihar Katsina ta yi watsi da korafe-korafen kungiyar, tare da jaddada cewa, tana ci gaba da ƙoƙarin magance dukkan matsalolin da suka shafi jami’ar da cigaban ilimi a jihar.
