Hon. Balele Aminu Dan Arewa, tare da Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, da ‘yan takarar Sanatoci da na Majalisar Wakilai ta Tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar APC, sun karɓi takardun Halastattun Yan takara daga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) domin tunkarar Babban Zaɓen Shekarar 2027.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, an gudanar da bikin miƙa takardun ne a Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, inda Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Dakta Bishir Gambo Saulawa, ya jagoranci gabatar da takardun ga ‘yan takarar wanda daga ciki har da Ɗantakarar Danmajalisar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Dutsinma da Kurfi, Hon. Aminu Balele Dan Arewa.
Da yake jawabi a lokacin, Hon. Dan Arewa ya bayyana muhimmancin haɗin kai da aiki tare tsakanin dukkan ‘yan takarar APC da shugabannin jam’iyyar domin tabbatar da nasara a zaɓen shekarar 2027.
Ya jaddada cewa, nasarar kowace jam’iyya tana dogara ne da haɗin kai, biyayya ga manufofin jam’iyya da kuma kusantar al’umma a matakin ƙasa da ma jihar Katsina da Kananan Hukumomin Dutsinma da Kurfi.
Tunda farko, ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki su guji duk wani abu da zai iya kawo rarrabuwar kawuna, tare da mayar da hankali wajen ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar domin nasarar su a shekarar 2027.
Haka kuma, Dan Arewa, ya kuma yi kira ga ‘yan takarar APC da magoya bayansu da su ci gaba da wayar da kan jama’a game da manufofi da shirye-shiryen jam’iyyar, tare da ƙara zage damtse wajen tattara goyon bayan al’umma tun daga matakin mazabu har zuwa ƙananan hukumomi na faɗin jihar baki ɗaya.
Ya yi nuni da cewa, tabbas gwamnatin APC a Katsina ta aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a fannoni daban-daban kamar tsaro, ilimi, lafiya, noma, samar da ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki, yana mai cewa waɗannan ayyuka za su ci gaba da zama ginshiƙin neman amincewar al’umma a zaɓen 2027.
