HomeSashen Hausa'Yan Jarida 128 Suka Halaka A Sassan Duniya A Shekarar 2025– Rahoto...

‘Yan Jarida 128 Suka Halaka A Sassan Duniya A Shekarar 2025– Rahoto IFJ

-

Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Ƙasa da Ƙasa (IFJ) ta ce jimillar ’yan jarida 128 aka kashe a fadin duniya a shekarar 2025, kuma fiye da rabinsu a yankin Gabas ta Tsakiya suke.

 

Sakataren Janar na IFJ, Anthony Bellanger, ya shaida wa AFP cewa wannan adadi mai muni, wanda ya karu daga na shekarar 2024, “ba wai kididdiga ba ce kawai, illa wani gargaɗin duniya ga abokan aikinmu.”

 

Ƙungiyar ta nuna damuwa musamman kan halin da ake ciki a yankunan Falasdinu, inda ta ce ta kiyaye mutuwar ’yan jarida 56 a shekarar 2025 yayin da yaƙin Isra’ila da Hamas ya ci gaba a Gaza.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Kwankwaso Na Nazarin Hada Kai da Atiku da Obi Domin Shiga ADC

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Jagoran New Nigeria People’s Party (NNPP), Sen Rabiu Musa Kwankwaso, na nazarin yiwuwar haɗa kai da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa...

Katsina Za Ta Karɓi Baƙuncin Mauludin Ƙasa na Inyass karo na Uku a Janairu 2026

An bukaci Gidan Rediyon Jihar Katsina da ya bayar da cikakken hadin kai da goyon baya wajen watsa dukkan ayyukan Mauludin Ƙasa na Inyass na...

Most Popular