HomeLabarai‎Malami Ya Zargi DSS da Tauye Masa ’Yancin Kare Kansa a Kotu

‎Malami Ya Zargi DSS da Tauye Masa ’Yancin Kare Kansa a Kotu

-

‎Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya zargi Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da daukar matakan hana shi cikakken ’yancinsa na shari’a da kare kansa yadda doka ta tanada.

‎A cikin wata sanarwa da Mai Taimaka Masa kan Harkokin Yaɗa Labarai, Mohammed Bello Doka, ya sanya wa hannu, Malami ya ce DSS na ci gaba da hana lauyoyinsa damar ganinsa, lamarin da ya hana shi tuntuba, ba da umarni, da kuma shirya takardun shari’a yadda ya dace.

‎Malami ya bayyana hakan a matsayin tauye hakkokin ɗan Adam, yana mai cewa irin waɗannan matakai sun sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya.

‎“Abin da ke faruwa ya nuna wani salo da ake fara kama mutum kafin bincike, sannan a fara neman hujjoji bayan tsare shi, wanda hakan ya saɓa doka da kuma ’yancin da kundin tsarin mulki ya tanada,” in ji sanarwar.

‎Ya ƙara da cewa abin damuwa ne matuƙa ganin yadda DSS ke aiwatar da abin da ya kira tsarewa, sannan neman hujjoji daga baya, yana mai jaddada cewa hakan barazana ce ga bin doka da oda ta ƙasa.

‎Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, DSS ba ta fitar da wata sanarwar martani kan zargin da tsohon Ministan ya yi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

An Kama Wasu Matasa Bisa Wani Aure Da Aka Daura Kan Sadakin N3,000 a Bauchi

Rahotanni daga Jihar Bauchi sun nuna cewa jami’an tsaro sun kama wasu matasa bayan wani aure da aka daura wa wasu matasa a kan sadakin...

NYCN Katsina: Leadership Dispute Emerges Over Planned State Tour

By Abubakar Haruna Mashi|Nigerian Post A leadership dispute has emerged within the National Youth Council of Nigeria (NYCN), Katsina State Chapter, following a request by the...

Most Popular